Sheikh al- Islaam Ibn Taimiyyah (R.A) ya ce:
"Wani lokaci Fasikanci yana kasancewa da barin Farillai, a wani lokaci kuma da aikata muharramai." (al-Imaan).
Sai ya lamarin ya kasance kamar haka: Mutum yana zama fasiki ne da hanyoyi masu yawa, amma idan ka tattare su za ka iske ba su fita gabarin abubuwa biyu (2) da Sheikh al-Islaam (R.A) ya ambata a sama ba:
1. Barin Farillai: Ba mafi girman farilla da take kan dan Adam sama da Kadaita Allah da bauta, domin shi ne mafi cancantarta daga wajen wanda ya kage su ba tare da wata bukata tasa koma bayan tasu ba, wannan shi ake nufi 'Tauhidi' wanda aka umarci kowace al'umma da cika bangarensa da imani da Manzon da aka tura mata. Duk wanda ya bar tauhidi ya bar mafi girman farilla, kuma hakan zai iya zama sanadiyyar dauwamarsa a cikin wuta, in ba ya tuba ta hanyar kadaita Allah (S.W.T) da bauta ba, kuma da cikakkiyar biyayya ga Sunnar Manzonsa (S.A.W).
Bugu da kari: Lallai Tauhidi shi ne mafi girman farilla take kan dan Adam, kaskanta shi kaskanta macikansa ne, kamar sallah da aka kira 'ginshikin addini' har zuwa jihadi da ya kasance 'kololuwarsa'.
Gini a kan haka: Ba babban fasiki sama da wanda ya bar kadaita Allah (S.W.T) da bauta ko ya tsammaci karantarwar Annabi (S.A.W) a kasa da karantarwar waninsa har ya zama yana gabatar da shi a kansa da Mahaliccinsa.
2. Aikata Muharramai: Hakika masu aikata abin da Allah (R.A) ya haramta sun rabu kashi biyu (2) kuma kowanne yana da hukuncin da ya cancance shi.
1. Mai aikata abin da aka haramta bisa ilmi: Lallai wannan ba shi da wani uzuri a wajen Allah (S.W.T) na rashin azabtarwa, amma idan ya ga dama zai iya gafarta masa, in kuma ya tuba shikenan, dama Allah mai yawan gafarwa ne, kuma mai yawan jin kai.
2. Mai aikata haramun bisa jahilci: Wannan lallai ba wani hukunci da zai sauka a kansa kafin isar ilmi a gare shi, saboda matashiyar da ake da ita a cikin Shari'ar Musulunci ta 'Uzuri da jahilci' wanda Khawarijawa da sauran kungoyoyin zafin kai.
La'akari da wannan sako za mu iya cewa: Lallai maganar Sheikh al-Islaam (R.A) tana alaka da banagere na farko ne daga cikin bangarorin masu aikata muharramai da suka gabata.
A wancan bangaren kenan, amma a wani bangare na daban babu aikin haramun wanda Allah (S.W.T) da Manzonsa (S.A.W) suka yi hani gabarinsa sama da hada shi da waninsa a cikin hakkinsa na cancantar bautawar bayinsa gare shi, irin wannan hali na sanya wa Allah (S.W.T) abokin tarayya ake kira 'Shirka', kuma a sakamakon yakarta aka aiko Manzanni (A.S), sa'annan a sakamakon yakarta aka aiyada su da mu'ujizozi domin tunkarar kangararrun mutane a cikin al'ummarsu da kwabarsu kana da bawa zuciyoyin masu saukin kai a cikinsu nutsuwa da hutu.
Kari a kan haka: Daga cikin abubuwan da suke cika kyawun kiyayya da shirka akwai yaki da bidi'ah; ita ce mafi girman kofar shiga sansanin shirka da zamani ya la'akarta tun tale-tale.
A matsayin takaicewa za mu iya cewa: Barin farillai zai iya kasancewa bisa abubuwa biyu kamar aikata muharramai daidai-wa-daida, saboda a karkashin aikata akasin abin da aka farlanta/wajabta ana tsintar ukubar aikata haram.
Kuma aikata muharramai matukar akwai lalura bai zama haramun ba, amma ita haramun ana kintata ta da iya matsayinta.
Misali: Kai ne kake Democracy bisa lalurar halin da ka tsinci kanka a cikinsa, sai matsayinka a cikin wannan batu ya kasance bai fita gabarin jefa kuri'a a ranarta ba, sa'annan ka jira sakamakonta, amma wanin haka haramun ne a gare ka, sai ya zama walima cin nasarar wannan zabe bata da gurbi a cikinsa, saboda ba yadda za a ce mutumin da ya tilastu zuwa ga cin mushe a sakamakon mafi rinjayen tunani da tsoron rasa rayuwarsa da zai yi, kuma a ce daga bisani ya zo yana walima a kan haka, sai a ce dama ya ci ne bisa radin kansa da wata kullalliya a zuciyarsa.
Sai ya zamanto mun samu hukuncin rashin halaccin fadadawa a kan lalura da wajabcin tsayawa a iya haddinta.
Saboda haka: Idan kana son zama salihi, sai ka nisanci sako-sako da al'amarin farillai, kuma ka rinka fadi-tashin saninsu a kullum a sakamakon kasancewar wajabcin haka a kanka, sa'annan ka lazimci taka-tsantsan da tsantsani gabarin aikata muharramai. A karkashin aikata haka wasunka suka amsa sunan Imani da Ihsani.
Allah sa mu wanye da rayuwar duniya lafiya.
Ibrahim Lawal Soro
14/11/2015 C.E
No comments:
Post a Comment