Ana yawan danganta mana shigarwa ko fitarwa daga cikin Salafiyyah, mabarnacin da ya fara yada wannan shubuha na yi masa martanin da ya kasa kalubalantarsa da gaskiya tun a 2014, to amma da yake har yanzu waccar guba da ya dasa tana yawo a jinanen wadanda suka kamu da ita, shi ne zan tsakuro wani sashi na abubuwan da na yi zayyana a wancan lokaci, amma da wasu sabin jumloli kamar haka:
-Sai ka ji suna cewa:
"Wane dan bidi'ah ne, wane ma dan bidi'ah!"
Dan uwa wannan kage ne daga wajenka a gare mu, ba mu bidi'anta wani daga cikin aljihunmu ba, amma muna nakalto cewa:
"Malam wane ya ce: wane Dan Bidi'ah ne, kuma ga dalilansa!
Misali: Sayyid Qutb da almajiransa"
To amma kai tsaye sai ka ga an jingina mana bidi'anta shi kai tsaye, yanzu wannan ba shi ba ne zalunci da rashin insafi da kuke yawan jifanmu da shi, ko an halasta muke ne?!
A takaice dai ya kamata a fahimci wannan batu mai zuwa:
Shiga Salafiyyah ko fita daga cikinta ayyukan zahiri ne suke hukunci a kan haka; duk wanda aka ce maka wannan Basalafe ne ko sabaninsa ayyukansa aka gani wadanda suka saba da wanda ta karantar, kuma gane haka aikin malamai ne, ba leken sirri aka yi masa ba, kamar yadda wasu mabartana suke ayyana wasu su leken sirri a kanmu, saboda haka abin da yake cikin zuciyar mutum ba ruwan kowa da shi, Allah (S. W. T) shi ne masanin abin da ya boyu da wanda ya bayyana, kuma wanda ya bayyana a kansa hukunci yake gudana, amma a wajenmu Mutane!
Allah ya raba mu da fitinar jahilci da zon zuciya!
©Ibrahim Lawal Soro
13. 11. 2017 C. E
No comments:
Post a Comment