Sheikh al-Islam Ibn Taimiyyah al-Harranee (Allah ya jikansa) ya ce:
"ﻭﻳﺠﺐ ﻋﻘﻮﺑﺔ ﻛﻞ ﻣﻦ ﺍﻧﺘﺴﺐ ﺇﻟﻲ ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺒﺪﻉ ﺃﻭ ﺫﺏ
ﻋﻨﻬﻢ ﺃﻭ ﺃﺛﻨﻲ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﺃﻭ ﻋﻈﻢ ﻛﺘﺒﻬﻢ ﺃﻭ ﻋﺮﻑ ﺑﻤﺴﺎﻋﺪﺗﻬﻢ
ﻭﻣﻌﺎﻧﺘﻬﻢ ﺃﻭ ﻛﺮﻩ ﺍﻟﻜﻼﻡ ﻓﻴﻬﻢ ﻭﺃﺧﺬ ﻳﻌﺘﺬﺭ ﻟﻬﻢ، ﺑﻞ ﺗﺠﺐ
ﻋﻘﻮﺑﺔ ﻛﻞ ﻣﻦ ﻋﺮﻑ ﺣﺎﻟﻬﻢ ﻭﻟﻢ ﻳﻌﺎﻭﻥ ﻋﻠﻲ ﺍﻟﻘﻴﺎﻡ ﻋﻠﻴﻬﻢ.
ﻭﺍﻟﻘﻴﺎﻡ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﻣﻦ ﺃﻭﺟﺐ ﺍﻟﻮﺟﺒﺎﺕ "
"Ya wajaba ayi ukuba (azaba) ga duk wanda ya jingina zuwa ga yan bidi'ah, ko ya kare su, ko ya yabe su, ko ya girmama littattafansu, ko an san shi da taimaka musu da tagaza musu, ko ya kyamaci magana akansu, ya kuma fara nema musu uzuri, kai ya ma wajaba a yi ukuba ga wanda ya san halinsu (amma) bai taimaka aka durkushe su ba, tsaiya akansu (domin duskurar da su) yana daga mafi wajabcin wajibai! " (1)
Na ce:
Bisa hasken abin da ya gabata za mu fahimci abubuwa kamar haka:
1- Hallacin ukuba ga wanda ya karkata ga yan bidi'a, ya jingina kansa da su, saboda hakan laifi ne, bai dace ga mai son tsira akan wani jirgi ya balla farfelarsa ba; ya saba wa hankali ga wanda ya ke son iya ruwa ya guntule hannayensa ba!
Wani mawaki ya ce:
"ترجو النجاة ولم تسلك مسالكها
ان السفينة لا تمشي على اليبس "
"Kai kake fatan ka yo tserewa
Ka ki bin hanyar wanyewa
Lallai bai tafiya bisa bushewa
Jirgin ruwa (bai tafiya akan yashi)"
Bidi'a sabo ce akwai mai kafirtawa
Bidi'a laifi ce mai fasikantarwa
Mai sabon Allah da Manzo yai tabewa
Manzon Allah (S. A. W) ya ce:
"من احدث في امرنا هذا ما ليس منه فهو رد"
"Duk wanda ya fari wani abu a cikin wannan Shari'a tamu, abin da (dama) ba ya daga cikinsa (balle ya kara raya shi) to kwansasshe ne (a gare shi) (2)
Bayan an wurga masa kayansa kuma ya cancanci ukuba, sababinta abubuwa ne masu yawa, daga ciki:
Allah ya ce:
"ﻓﻠﻴﺤﺬﺭ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻳﺨﺎﻟﻔﻮﻥ ﻋﻦ ﺃﻣﺮﻩ ﺃﻥ ﺗﺼﻴﺒﻬﻢ ﻓﺘﻨﺔ ﺃﻭ ﻳﺼﻴﺒﻬﻢ ﻋﺬﺍﺏ ﺃﻟﻴﻢ"
"Wadanda suke kaucewa gabarin umarninsa, su ji tsoro (su shiga taitayinsu), don kar wata masifa ta same su ko wata azaba mai radadi" (3)
Kirkirar wani abu a cikin Shari'ah ko shigowa da wani kirkirarre daga waje tare da nema masa matsuguni saba wa umarnin Allah ne, saboda haka ya cancanci azabtarwa.
al-Allaamah al-Mufassir al-Usuulee Muhammad al-Amin al-Shanqeetee (R. A) dangane da ma'anar wannan aya ya ce:
"ﻭَﻫَﺬِﻩِ ﺍﻟْﺂﻳَﺔُ ﺍﻟْﻜَﺮِﻳﻤَﺔُ ﻗَﺪِ ﺍﺳْﺘَﺪَﻝَّ ﺑِﻬَﺎ ﺍﻟْﺄُﺻُﻮﻟِﻴُّﻮﻥَ ﻋَﻠَﻰ ﺃَﻥَّ
ﺍﻟْﺄَﻣْﺮَ ﺍﻟْﻤُﺠَﺮَّﺩَ ﻋَﻦِ ﺍﻟْﻘَﺮَﺍﺋِﻦِ ﻳَﻘْﺘَﻀِﻲ ﺍﻟْﻮُﺟُﻮﺏَ ; ﻟِﺄَﻧَّﻪُ - ﺟَﻞَّ
ﻭَﻋَﻠَﺎ - ﺗَﻮَﻋَّﺪَ ﺍﻟْﻤُﺨَﺎﻟِﻔِﻴﻦَ ﻋَﻦْ ﺃَﻣْﺮِﻩِ ﺑِﺎﻟْﻔِﺘْﻨَﺔِ ﺃَﻭِ ﺍﻟْﻌَﺬَﺍﺏِ
ﺍﻟْﺄَﻟِﻴﻢِ ، ﻭَﺣَﺬَّﺭَﻫُﻢْ ﻣِﻦْ ﻣُﺨَﺎﻟَﻔَﺔِ ﺍﻟْﺄَﻣْﺮِ ، ﻭَﻛُﻞُّ ﺫَﻟِﻚَ ﻳَﻘْﺘَﻀِﻲ
ﺃَﻥَّ ﺍﻟْﺄَﻣْﺮَ ﻟِﻠْﻮُﺟُﻮﺏِ ، ﻣَﺎ ﻟَﻢْ ﻳَﺼْﺮِﻑْ ﻋَﻨْﻪُ ﺻَﺎﺭِﻑٌ ؛ ﻟِﺄَﻥَّ ﻏَﻴْﺮَ
ﺍﻟْﻮَﺍﺟِﺐِ ﻟَﺎ ﻳَﺴْﺘَﻮْﺟِﺐُ ﺗَﺮْﻛُﻪُ ﺍﻟْﻮَﻋِﻴﺪَ ﺍﻟﺸَّﺪِﻳﺪَ ﻭَﺍﻝﺗَّﺤْﺬِﻳﺮ"
"Wannan aya mai girma masana Usuul al-Fiqh sun kafa dalili da ita akan cewa: Lallai umarni tobabbe daga wasu manuna (ga sabaninsa) yana fa'idantar da wajabci, saboda Shi (Mabuwayi da daukaka) ya alkawarta fitina da azaba mai radadi ga wadanda suka saba wa umarninsa, kana ya yi musu gargadi gabarin saba wa umarnin, dukkan wancaninka yana nuna umarni(in) yana fa'idantar da wajabci, matukar wani mai juyarwa bai juya (akalarsa) gabarinsa ba!
Saboda koma bayan wajibi barinsa ba ya kokarin wajabtar da azaba mai radadi da tsoratarwa" (4)
Yana da kyau mu sani: barin wajibi yana daga cikin abubuwan da suke haifar da haramci. Wanda ya aikata haram kuma mai iya fuskantar ukuba ce in bai tuba ba!
Bisa abin da ya ke sama ba bu wani haram mai kyau kamar yadda ba bu wata bidi'ah mai kyau.
Ibn al-Maashijuun (R. A) ya ce:
"ﺳﻤﻌﺖ ﻣﺎﻟﻜًﺎ- ﺭﺣﻤﻪ ﺍﻟﻠﻪ - ﻳﻘﻮﻝ : " ﻣﻦ ﺍﺑﺘﺪﻉ ﻓﻲ
ﺍﻹﺳﻼﻡ ﺑﺪﻋﺔً ﻳﺮﺍﻫﺎ ﺣﺴﻨﺔ ﻓﻘﺪ ﺯﻋﻢ ﺃﻥ ﻣﺤﻤﺪًﺍ ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ
ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ﺧﺎﻥ ﺍﻟﺮﺳﺎﻟﺔ، ﻷﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻳﻘﻮﻝ: ( ﺍﻟﻴﻮﻡ ﺃﻛﻤﻠﺖ
ﻟﻜﻢ ﺩﻳﻨﻜﻢ ) ( ﺍﻟﻤﺎﺋﺪﺓ3/ ) ﻓﻤﺎ ﻟﻢ ﻳﻜﻦ ﻳﻮﻣﺌﺬ ﺩﻳﻨًﺎ ﻓﻼ
ﻳﻜﻮﻥ ﺍﻟﻴﻮﻡ ﺩﻳﻨًﺎ"
"Na ji Maalik (R. A) yana cewa: "Duk wanda ya kirkiri wata bidi'ah a cikin addini da ya ke ganin tana da kyau, hakika ya raya cewa (Annabi) Muhammad (S. A. W) ya ha'inci manzanci, Saboda Allah yana cewa: " A yau ne na cika muku addininku" (al-Maa'idah:3), (saboda haka) abin da bai zama addini a wancan kwanaki ba, a yau ba zai zama addini ba!" (5)
2- Mun fahimci rashin hallacin kare yan bidi'ah da yabon littattafansu, saboda abin da ya ke cikin haka na taimaka wa barna da ma'abotanta, alhali an hane mu gabarin haka.
Allah (S. W. T) ya ce:
"وتعانوا على البر والتقوى ولا تعاونوا على الاثم والعدوان"
"Ku yi taimakekkeniya akan biyayya wa Allah, kar ku yi taimakekkeniya akan sabo da ketare iyaka" (6)
kirkirar bidi'ah, aiki da ita, da taimaka wa ma'abocinta sabo ne, kuma ketare iyaka ce: mai aikata daya daga cikinsu bai tsaya a yadda aka umarce shi ba!
An tambayi al-Allaamah Salih al-Fauzaan (H.A) dangane da karanta littattafan yan bidi'ah da sauraren kasusuwansu, sai ya amsa da cewa:
"ﻻﻳﺠﻮﺯ ﻗﺮﺍﺀﺓ ﻛﺘﺐ
ﺍﻟﻤﺒﺘﺪﻋﺔ ﻭﻻﺳﻤﺎﻉ ﺍﺷﺮﻃﺘﻬﻢ ﺍﻻ ﻟﻤﻦ
ﻳﺮﻳﺪ ﺃﻥ ﻳﺮﺩ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﻭﻳﺒﻴﻦ ﺿﻼﻟﻬﻢ "
"Ba ya halatta karanta littattafan yan bidi'ah ko saurarar kasusuwansu sai ga wanda yake nufin martani gare su da bayyana batarsu" (7)
Dan uwa mai girma, abin da maganar al-Allaamah ta kunsa a fili yake; ba zancen bada kariya ma ga littattafansu ba, wanda rashin anfaninsa a fili yake, har karatun da mai yiwuwa ka samu wata fa'ida bai halatta ba, sai dai in za ka tsayu da yin martani.
Bugu da kari, in wata fa'ida ce kake nema, kamar yadda malamai suka ce: za ka iya samunta a littattafan ahlu al-Sunnah cikin aminci.
Na taba karanta maganar al-Allaamah Uthaimeen amma bill-hakika na manta yadda na karanta ta, amma na fi tsammaninta a cikin "كتاب العلم-- Littafin Ilmi" ya ke cewa: Daliban ilmi su nisanci littattafan yan bidi'ah, sai ya yi misali da tafsirin al-Zamakhsharee ya ce: Mu'utazilanci ya narke a cikinsa ta yadda har cikin malamai ba kowa ne zai iya ganowa ba, balle dalibin ilmi.
Haka ma'abota son zuciya suke, sun iya narkar da dafinsu a karkashin yawunsu, mafi girman misali anan fage shi ne: Sayyid Qubt sai almajirinnsa Muhammad Hassan; wanda khawarijanci a wani bangare, da sufanci a wani bangare na daban suka yi lif-lif a karkashin alkalaminsa da kalmominsa.
Misali: Ware "التوحيد الحاكمية" da ya yi da ambato sabanin abin da ahl Al-Sunnah suke kai, tare da ballewa zuwa ga halaccin fito wa shugabannin da ba sa hukunci da Shari'ar musulunci, za ka iya samun wani sashi na irin wadannan maganganu a cikin littafinsa "حقيقة التوحيد" da maganganunsa bayan "al-Thaurah" (8)
al-Allaamah Uthaimeen ya yi martani da rotse ga ire-irensa; wadanda suka zakalkale sai sun fige Haakimiyyah daga Uluuhiyyah, za ka iya duba "فتاوى العقيدة-Fatawowin Akida" wadanda aka hada bayan rasuwarsa -Allah ya jikansa.
Kari akan haka; yabon dan bidi'ah taimako ne da kara ingiza shi cikin kwaroron bata, irin haka ba halin mutanen kirki ba ne!
Manzon Allah (S.A.W) ya ce:
"ﻣﻦ ﺭﺃﻯ ﻣﻨﻜﻢ ﻣﻨﻜﺮﺍ ﻓﻠﻴﻐﻴﺮﻩ
ﺑﻴﺪﻩ ، ﻓﺈﻥ ﻟﻢ ﻳﺴﺘﻄﻊ ﻓﺒﻠﺴﺎﻧﻪ ، ﻓﺈﻥ ﻟﻢ ﻳﺴﺘﻄﻊ ﻓﺒﻘﻠﺒﻪ ،
ﻭﺫﻟﻚ ﺃﺿﻌﻒ ﺍﻹﻳمان"
"Duk wanda ya ga wani abin ki (munmuma)sai ya kawar da shi da hanunsa, in ba zai iya ba, (to) da harshensa, in ba zai iya ba, (to) zuciyarsa, kuma shi ne mafi raunin imani" (9)
al-Allaamah Uthaimeen (R. A) a cikin sharhin wannan hadisi ya ce:
"ﻭﻗﻮﻟﻪ : " ﻣَﻦْ ﺭَﺃَﻯ" ﻫﻞ ﺍﻟﻤﺮﺍﺩ ﻣﻦ ﻋﻠﻢ ﻭﺇﻥ ﻟﻢ ﻳﺮَ
ﺑﻌﻴﻨﻪ ﻓﻴﺸﻤﻞ ﻣﻦ ﺭﺃﻯ ﺑﻌﻴﻨﻪ ﻭﻣﻦ ﺳﻤﻊ ﺑﺄﺫﻧﻪ ﻭﻣﻦ
ﺑﻠﻐﻪ ﺧﺒﺮ ﺑﻴﻘﻴﻦ ﻭﻣﺎ ﺃﺷﺒﻪ ﺫﻟﻚ، ﺃﻭ ﻧﻘﻮﻝ : ﺍﻟﺮﺅﻳﺎ
ﻫﻨﺎ ﺭﺅﻳﺔ ﺍﻟﻌﻴﻦ، ﺃﻳﻬﻤﺎ ﺃﺷﻤﻞ؟
ﺍﻟﺠﻮﺍﺏ : ﺍﻷﻭﻝ،ﻓﻴﺤﻤﻞ ﻋﻠﻴﻪ،ﻭﺇﻥ ﻛﺎﻥ ﺍﻟﻈﺎﻫﺮ
ﺍﻟﺤﺪﻳﺚ ﺃﻧﻪ ﺭﺅﻳﺔ ﺍﻟﻌﻴﻦ ﻟﻜﻦ ﻣﺎﺩﺍﻡ ﺍﻟﻠﻔﻆ ﻳﺤﺘﻤﻞ
ﻣﻌﻨﻰ ﺃﻋﻢ ﻓﻠﻴﺤﻤﻞ ﻋﻠﻴﻪ "
"Kuma fadinsa: "wanda ya gani" shin manufar ita ce wanda ya sani koda bai gani ba, sai ya kunshi wanda ya gani da wanda ya ji da kunnensa, da wanda labari ya iske shi bisa yakini, da abin da ya yi kama da wannan, ko za mu ce: gani anan ganin ido ne, wanne daga cikin biyun ya fi gamewa?!
Amsa (kuma akan haka) ita ce: Daga farko, za a dauke (shi akan wannan ma'ana), koda zahirin hadisin ganin ido (ya ke nufi), sai dai matukar lafazin (hadisin) yana kunshe akan gamammiyar ma'ana sai a dora shi (akanta).
Ya kara da cewa:
"ﻭﻗﻮﻟﻪ : " ﻣُﻨْﻜَﺮﺍً" ﺍﻟﻤﻨﻜﺮ :ﻫﻮ ﻣﺎ ﻧﻬﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻪ
ﻭﺭﺳﻮﻟﻪ، ﻷﻧﻪ ﻳﻨﻜﺮ ﻋﻠﻰ ﻓﺎﻋﻠﻪ ﺃﻥ ﻳﻔﻌﻠﻪ .
"Da fadinsa: "Abin ki" shi abin ki (shi ne): dukkan abin da Allah ya yi hani da manzonsa gabarinsa, saboda (musanta)wa mai aikata shi aikata shi"
Ya dora da cewa:
" ﻓَﻠْﻴُﻐَﻴِّﺮْﻩُ" ﺃﻱ ﻳﻐﻴﺮ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﻤﻨﻜﺮ ﺑﻴﺪﻩ .
ﻣﺜﺎﻟﻪ : ﻣﻦ ﺭﺃﻯ ﻣﻊ ﺷﺨﺺ ﺁﻟﺔ ﻟﻬﻮ ﻻ ﻳﺤﻞ
ﺍﺳﺘﻌﻤﺎﻟﻬﺎ ﺃﺑﺪﺍً ﻓﻴﻜﺴﺮﻫﺎ "
"Sai ya sauya shi" ai ya sauya wannan munmuna da 'hanunsa'. Misalinsa: Duk wanda ya ga wani mutun da kayan wargi da ba ya halatta a yi anfani da shi har abada sai ya karya shi"
Ya ci gaba:
"ﻭﻗﻮﻟﻪ : " ﻣُﻨْﻜَﺮَﺍً " ﻻﺑﺪ ﺃﻥ ﻳﻜﻮﻥ ﻣﻨﻜﺮﺍً ﻭﺍﺿﺤﺎً ﻳﺘﻔﻖ
ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺠﻤﻴﻊ، ﺃﻱ ﺍﻟﻤﻨﻜﺮ ﻭﺍﻟﻤﻨﻜﺮ ﻋﻠﻴﻪ،ﺃﻭ ﻳﻜﻮﻥ
ﻣﺨﺎﻟﻔﺔ ﺍﻟﻤﻨﻜﺮ ﻋﻠﻴﻪ ﻣﺒﻴﻨﺔ ﻋﻠﻰ ﻗﻮﻝ ﺿﻌﻴﻒ ﻻ
ﻭﺟﻪ ﻟﻪ .
ﺃﻣﺎ ﺇﺫﺍ ﻛﺎﻥ ﻣﻦ ﻣﺴﺎﺋﻞ ﺍﻻﺟﺘﻬﺎﺩ ﻓﺈﻧﻪ ﻻ ﻳﻨﻜﺮﻩ ."
"Fadinsa: "wani abin ki" ba makawa ya kasance abin ki a fayyace , a yayin da dukkan mutane suka hadu akansa, ana nufin abin ki da wanda ake kiye masa, ko ta kasance sabawar wanda ake kiye masa ginanniya ce akan dalili mai raunin da bashi da wata fuska (ta inganci), amma idan akan mas'alolin ijtihadi ne ba za a kiye masa ba (ba za a musanta masa shi ba!)
Ya kara akan wancan da:
" ﻓَﺈِﻥْ ﻟَﻢْ ﻳَﺴْﺘَﻄِﻊْ" ﺃﻱ ﺇﻥ ﻟﻢ ﻳﺴﺘﻄﻊ ﺃﻥ ﻳﻨﻜﺮﻩ ﺑﻴﺪﻩ
" ﻓَﺒِﻠِﺴَﺎﻧِﻪِ " ﺃﻱ ﻓﻠﻴﻨﻜﺮﻩ ﺑﻠﺴﺎﻧﻪ ﻭﻳﻜﻮﻥ ﺫﻟﻚ :
ﺑﺎﻟﺘﻮﺑﻴﺦ،ﻭﺍﻟﺰﺟﺮ ﻭﻣﺎ ﺃﺷﺒﻪ ﺫﻟﻚ،ﻭﻟﻜﻦ ﻻﺑﺪ ﻣﻦ
ﺍﺳﺘﻌﻤﺎﻝ ﺍﻟﺤﻜﻤﺔ، ﻛﻤﺎ ﺳﻴﺄﺗﻲ ﻓﻲ ﺍﻟﻔﻮﺍﺋﺪ ﺇﻥ ﺷﺎﺀ
ﺍﻟﻠﻪ"
"In ba shi da damar haka; musanta shi da hanunsa, (to) sai ya yi da "harshensa" hakan kuma ya kasance da: kwalewa da tsawatarwa (akan aikinsa) amma ba makawa anfani da hikima, kamar yadda zai zo a cikin fa'idoji, in sha Allah. "
A karshe ya ce"
"ﻭﻗﻮﻟﻪ "ﺑِﻠِﺴَﺎﻧِﻪِ " ﻫﻞ ﻧﻘﻴﺲ ﺍﻟﻜﺘﺎﺑﺔ ﻋﻠﻰ
ﺍﻟﻘﻮﻝ؟
ﺍﻟﺠﻮﺍﺏ : ﻧﻌﻢ، ﻓﻴﻐﻴﺮ ﺍﻟﻤﻨﻜﺮ ﺑﺎﻟﻠﺴﺎﻥ، ﻭﻳﻐﻴﺮ
ﺑﺎﻟﻜﺘﺎﺑﺔ، ﺑﺄﻥ ﻳﻜﺘﺐ ﻓﻲ ﺍﻟﺼﺤﻒ ﺃﻭ ﻳﺆﻟﻒ ﻛﺘﺒﺎً
ﻳﺒﻴﻦ ﺍﻟﻤﻨﻜﺮ .
" ﻓَﺈﻥْ ﻟَﻢْ ﻳَﺴﺘَﻄِﻊْ ﻓَﺒِﻘَﻠْﺒِﻪِ" ﺃﻱ ﻓﻠﻴﻨﻜﺮ ﺑﻘﻠﺒﻪ، ﺃﻱ
ﻳﻜﺮﻫﻪ ﻭﻳﺒﻐﻀﻪ ﻭﻳﺘﻤﻨﻰ ﺃﻥ ﻟﻢ ﻳﻜﻦ .
" ﻭَﺫَﻟِﻚَ" ﺃﻱ ﺍﻹﻧﻜﺎﺭ ﺑﺎﻟﻘﻠﺐ " ﺃَﺿْﻌَﻒُ ﺍﻹِﻳْﻤَﺎﻥِ " ﺃﻱ
ﺃﺿﻌﻒ ﻣﺮﺍﺗﺐ ﺍﻹﻳﻤﺎﻥ ﻓﻲ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﺒﺎﺏ ﺃﻱ ﻓﻲ
ﺗﻐﻴﻴﺮ ﺍﻟﻤﻨﻜﺮ "
"Fadinsa: "Harshensa" shin za mu kiyasta rubutu akansa?
Amsa: Na'am, sai a sauya abin ki da harshe, haka kuma da rubutu, kamar ya yi rubutu a jaridu ko ya wallafa littafi yana bayyana munkarin.
"In ba zai iya ba, (to) da zuciyarsa" ai ya kiyace shi da zuciyarsa, ya ki shi, ya kyamace shi, ya yi ta fatan da ma bai kasance ba (ba a yi shi ba), "haka kuma" ai kin nasa (musanta) da zuciyar shi ne mafi raunin matakan imani a wannan babi; babin sauya munmuna" (8)
A hasken abin da ya ke sama mun fahimci wajabcin kawar da munmuna akan kowa gwargwadon iko da damar da ya samu.
Tare da kasancewar kawar da 'abin ki' (munmuna) da zuciya shi ne mataki na karshe a wannan babi, amma yana da wasu iyakoki da ya zama wajibi a kiyaye su:
-Fatan ina ma da abin bai dandani rayuwa ba,
-Kiyayya da 'abin' da mai aikata shi,
-Gyamatarsa da ma'abocinsa da
- Nisantar wajen da ake yinsa.
Kun ga mai yabon dan bidi'ah ya saba wa duk abin da ya gabata.
Shi yasa masu irin wannan aika-aika suna da wata illa ta musamman: wani lokaci za ka ji suna cewa: dole mu tausasawa wanda ya saba, dan bidi'ah kuma suke nufi.
Wannan shi ake nufi da 'ruwantar da manhajin ahl al-Sunnah - تمييع منهج اهل السنة والجماعة' ta yadda wasu da sunan sunnah suke halakar da sunnah.
Sheikh al-Islam ya ce:
"ﻓﻼﺑﺪ ﻣﻦ ﺍﻟﺘﺤﺬﻳﺮ ﻣﻦ
ﺗﻠﻚ ﺍﻟﺒﺪﻉ ﻭﺍﻥ ﺍﻗﺘﻀﻰ ﺫﻟﻚ ﺫﻛﺮﻫﻢ ﻭﺗﻌﻴﻴﻨﻬﻢ ) ﻭﻗﺎﻝ
ﺗﻠﻤﻴﺬﻩ ﺍﻟﺒﺎﺭ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺍﺑﻦ ﺍﻟﻘﻴﻢ : « ﻣﻦ ﻧﺼﺮ ﻫﻮﺍﻩ ﻓﺴﺪ ﻋﻠﻴﻪ
ﻋﻘﻠﻪ ﻭﺭﺃﻳﻪ ﻷﻧﻪ ﻗﺪ ﺧﺎﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻲ ﻋﻘﻠﻪ ﻓﺄﻓﺴﺪﻩ ﻋﻠﻴﻪ
ﻭﻫﺬﺍ ﺷﺄﻧﻪ ﺳﺒﺤﺎﻧﻪ ﻭﺗﻌﺎﻟﻰ ﻓﻲ ﻛﻞ ﻣﻦ ﺧﺎﻧﻪ ﻓﻲ ﺃﻣﺮ ﻣﻦ
ﺍﻷﻣﻮﺭ ﻓﺈﻧﻪ ﻳﻔﺴﺪﻩ ﻋﻠﻴﻪ"
"Ba bu makawa daga razanarwa gabarin dukkan wadancan bidi'o'in koda haka zai hukunta kiransu (kiran ita bidi'ar da ma'abotanta) da aibata su.
Almajirinsa mai biyayyan nan al-Imam Ibn al-Qayyim ya ce: " Duk wanda ya taimaki son zuciyarsa zai bata masa hankalinsa da ra'ayinsa, saboda ya rigaya ya ha'inci Allah, shi ma sai ya bata masa shi a gare shi, wannan sha'aninsa ne (S. W. T), duk wanda ya ha'ince shi a cikin wani al'amari daga cikin al'amura lallai yana bata masa shi a gare shi." (9)
Saboda haka wadanda suka karkace gabarin karantarwar gaske suke zama ya kasge; taburburi ne aikinsu.
3- Neman uzuri gare su bai halatta ba, saboda sun gina al'amuransu ne tun farko akan son zuciya, wanda ya biye zuciya ita ya ke gani a gabansa, in da wata farar gaskiya za ta wuce ta gabansa, sai ya yi iya kokari domin ta saje da bakar zuciyarsa. Za ka fahimci haka idan ka yi dubi zuwa ga wainar da suke toyawa da ayoyin Allah (S. W. T) da hadisan manzonsa (S. A. W).
A karkashin wannan magabata na kwarai ake nema wa uziri, daga kan sahabban manzon Allah (R. A) zuwa kan wadanda suka biyo su da kyautatawa, amma yan ra'ayin kangarewa akansa tare da karkacewarsa, rashin tubarsu bisa karantar Shari'ah ba bu wani uzuri a wajen ahl al-Sunnah gare su bayan cikar sharuda da gushewar masu hanawa.
Wannan kuma shi ya bambance su da al-Haddaadiyyah (الحدادية) mabiya Mahmud al-Haddaad al-Misree; wadanda suke yaki da uzuri da jahilci, a jahilci da zagewarsu ga manhajin khawaarij ba sa ganin bambanci a tsakanin Ibn Hajar al-Asqalaanee da Jahm dan Safwaan. Wannan tsarinsu kenan, Allah wadai da shi.
A wani bangare daban kuma sai aka samu 'Yan Ruwantarwa' (الممييعة ) wadanda suka fi karfi a karkashin Ali al-Halabee; meman uzurinsu ya wuce gona da iri, bal dimuwa da ta ke gabansu maras iyaka ce! Ba su zam salafawa ba, ba su zam haddaadiyawa da cikakkiyar siffa ba, bal kusancinsu da Haddaadiyyah ya fi karfi sama da Salafiyyah, bal sun dara su a lokuta mafi dama, saboda sunan salafiyyah shi ne a bakinsu, har wasu marassa ganewa ke ganinsu Salafawa!
Ibn al-Muhalhal(hil) (R. A) ya ce:
"ﻟﻮ ﻛﺎﻥ ﺻﺎﺣﺐ ﺍﻟﺒﺪﻋﻪ ﺍﺫﺍ
ﺟﻠﺴﺖ ﺍﻟﻴﻪ ﻳﺤﺪﺛﻚ ﺑﺒﺪﻋﺘﻪ ﺣﺬﺭﺗه ﻭﻓﺮﺭﺕ ﻣﻨﻪ ﻭﻟﻜﻨه
ﻳﺤﺪﺛﻚ ﺑﺄﺣﺎﺩﻳﺚ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﻓﻲ ﺑﺪﻭ ﻣﺠﻠﺴﻪ ﺛﻢ ﻳﺪﺧﻞ ﻋﻠﻴﻚ
ﺑﺪﻋﺘﻪ ﻓﻠﻌﻠﻬﺎ ﺗﻠﺰﻡ ﻗﻠﺒﻚ ﻓﻤﺘﻰ ﺗﺨﺮﺝ ﻣﻦ ﻗﻠﺒﻚ"
"In da dan bidi'ah (a karon farko) idan ka zauna a wajensa ya baka labarin bidi'arsa zaka tsorace ci shi (ka fadaka da shi), ka kudu daga wajensa, sai dai (saboda makircinsa) sai ya rinka baka labarin sunnah a farkon zamansa (da kai), sa'annan ya shi go maka da bidi'arsa watakila ta lazimci zuciyarka, (to) a irin wannan yanayi yaushe za ta fita daga zuciyarka?! "
Wannan shi ne halin 'Yan Ruwantarwa' da mafi girman wadanda suke yabonsu tare da kare su, kamar al-Ikhwan al-Muslimun da yayansu, jikanu, da tattaba kunnensu.
Abin mamaki, a karkashin wannan batar tasu, akwai wanda ya ke ganin Jahm dan Safwaan: kartikin al-Jahmiyyah (الجهمية ) ba dan bidi'ah ba ne.
Allah kare mu daga bata bayan shiriya.
4- A karkashin maganarsa har ilau mun ga cewa dankwafe yan bidi'ah yana daga cikin mafi wajabcin wajibai, hakan kuma ya kasance ne a sakamakon abubuwa masu yawa, daga cikinsu akwai:
A- Shi kansa datarwa ce ta ubangiji da kuma horewarsa, wani ya mallaki kayan aikin da za a fafata da shi, amma bai mallaki karfin hakan ba!
B- Aiki ne da ma'abotansa suka fi kowa yawan makiya da mahassada; galibin mutane kuma sun fi fifita maslahar kansu akan ta addininsu.
C- Rashin makamin fita filin daga a bangaren mafi yawan wadanda suke da kishin addini.
Ibn Qudaamah al-Maqdisee (R. A) ya ce:
" ﻭﻣﻦ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﻫﺠﺮﺍﻥ ﺃﻫﻞ
ﺍﻟﺒﺪﻉ ﻭﻣﺒﺎﻳﻨﺘﻬﻢ ﻭﺗﺮﻙ ﺍﻟﺠﺪﺍﻝ ﻭﺍﻟﺨﺼﻮﻣﺎﺕ ﻓﻲ ﺍﻟﺪﻳﻦ
ﻭﺗﺮﻙ ﺍﻟﻨﻈﺮ ﻓﻲ ﻛﺘﺐ ﺍﻟﻤﺒﺘﺪﻋﺔ ﻭﺍﻹﺻﻐﺎﺀ ﺇﻟﻰ ﻛﻼﻣﻬﻢ
ﻭﻛﻞ ﻣﺤﺪﺛﺔ ﻓﻲ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﺑﺪﻋﺔ"
"Yana daga (cikin akida ta sunnah) kaura ce masa, da saba musu, da barin jayayya da husuma a cikin addini.
(yana daga cikin sunnah) barin kallon littattafan yan bidi'ah (karanta su) da sauraren maganarsu, kuma kowane kagaggen abu a cikin addinin (musulinci) bidi'ah ce (kuma kowace bidi'ah bata ce). (10)
A karkashin wannan magana nake cewa:
Batun jidali, husuma, da mukabala da yan bidi'ah wanda magabata na kwarai suka tsoratar gabarinsa, suka yi hani akansa, a wannan lokaci namu ya zama ruwan dare, bal ya zama gudumar da daliban da ba su fahimci komai a manhajin magabata na kwarai ba balle kwadunan kejunansu, domin fitowa farfajiyar shahara da bani na iya.
Abin da muka san magabata sun fara sanuwa da shi: karantarwa ce ba yawon mukabala da munazara a gidajen yan bidi'ah ba! Alheri daga yadda kake za ka tsarkake niyya ka aika shi, sai ya isa yadda kafarka ba za ta yi fatan zuwa ba, saboda matsatsi da surkukukinsa.
al-Allaamah al-Albanee daga Maktabah al-Dhahiriyyah alherinsa ya isa garin wahayi har aka gayyace shi domin ci gaba da hidima ga wahayi.
An samu wani dan Ibaatiyyah da ya bukaci munazara da Bin Baz a Haramin Makkah ko Madinah akan batu kamar haka: Shin al-Halittacce Ne Ko Akasin Haka?!
al-Imaam Bin Baaz ya ki amince masa, saboda dalilai kamar haka:
i-Dan bidi'ah wulakantacce ne, ba shi da wata daraja, saurararsa a irin wannan yanayi nasa kara martaba shi ne. Musamman wata katuwar bidi'ah zai zo karewa, wacce irin su Imaam Ahmad (R. A) suka kafirta ma'abocinta bayan an sun tsaida masa hujja.
ii-Ya fahimci burinsa shahara da shi, sai ya ki; hasken shuhurar da ya ke so ya dandana a jikinsa ya haramta masa.
Lallai bin tafarkin magabata na kwarai akwai kariya mai girma a cikinsa.
Zai anfanar in muka buga misali, saboda da shi ne wasu abubuwan ke kara bayyana.
A kaduna akwai wani da ake kira Mal. Musa Asadussunnah, na san shi tun shekara da bakwai da suka shige a shagalce da mukabala da yan shi'ah, ya shahara akan haka, in da za ka tuntubi wani na da haka zai fada maka: " Na san shi ne ta hanyar mukabala."
Ban wuce shekara biyu da saninsa ba na fahimci yadda bawan ya dosa; neman shuhura ta hanyar tunkarar yan bidi'ah da mukabala, koda kuwa hasarar da za ta biyo baya tafi ribar yawa da sauran tasiri, kuma a mafi yawan zaman nasu hasara ta fi yawa!
A wajejen 2010-2011na je Kaduna domin wani littafina da zan mika wa Publisher, sai na biya ta gidan wani abokina na kwana, kashegari ina kokarin hada yan komatsaina shi kuma yana kokarin tattaro min wani kaset, kamar yadda ya fada min: "Wani kaset zan baka, ina fatan za ka anfana da shi?!."
"In sha Allah." Na amsa masa da girmamawa, saboda yana gaba da ni sosai, sha'anin zaman makaranta ne ya hada ni da shi.
A cikin bakar leda ya sanya kaset din, bayan na shiga yar kurkurar mutan nan da ake Kabu-kabu da ita izuwa bakin babban titi daga unguwar Dosa da ya ke, sai na yi yunkurin budewa, amma ban samu dama ba sai da na hau wata Bus zuwa KadPoly da ta ke Tudun Wada, anan ne na ga Suna da hoton Musa Asadussunnah da Umar Shehu, sai na ce:
"Bawan Allah kai ne anan, ba kuma mukabala ka zo ba, domin bisa kyautata tsammani shi ma wannan mai . . . "
A takaice, ahl al-Sunnah ba sa barin wani dan bidi'ah Ya shahara da su ko su shahara da dan bidi'ah kamar yadda al-Qaasim Hotoro ya shahara da Abduljabbar.
al-Imaam al-Laalikaa'i (R. A) ya ce:
"ﻓﻤﺎ ﺟﻨﻰ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ ﺟﻨﺎﻳﺔ
ﺃﻋﻈﻢ ﻣﻦ ﻣﻨﺎﻇﺮﺓ ﺍﻟﻤﺒﺘﺪﻋﻪ , ﻭﻟﻢ ﻳﻜﻦ ﻟﻬﻢ ﻗﻬﺮ ﻭﻻ ﺫﻝ
ﺃﻋﻈﻢ ﻣﻤﺎ ﺗﺮﻛﻬﻢ ﺍﻟﺴﻠﻒ ﻋﻠﻰ ﺗﻠﻚ ﺍﻟﺠﻤﻠﺔ ﻳﻤﻮﺗﻮﻥ ﻣﻦ
ﺍﻟﻐﻴﻆ ﻛﻤﺪﺍ ﻭﺩﺭﺩﺍ , ﻭﻻﻳﺠﺪﻭﻥ ﺍﻟﻰ ﺍﻇﻬﺎﺭ ﺑﺪﻋﺘﻬﻢ ﺳﺒﻴﻼ . . . "
"Ba a yi wa musulunci aika-aika mafi girmanta sama da munazara da yan bidi'ah ba, wani karfi ko kaskanci bai taba kasancewa nasu ba, koma bayan wanda magabata na kwarai suka bar su akansa, bisa wancar jumla (da ambatonta ya gabata), suna mutuwa bisa kunci; (tare da matsanincin) fushi da takunkumi, saboda ba sa samun hanyar da za su bayyana bidi'arsu." (11)
Da irin wannan salo ne magabata na kwarai suka lullube bakunan wadanda suka fi Jahm dan Safwaan Sharri.
Shi ya sa a lokacin da Shaidanin nan ya bayyana: Muhammad Yusuf ya kokarta sai ya yi mukabala da Sheikh Ja'afar a kara haskaka tauraruwarsa, sai Sheikh (R. A) ya ki, domin ya gano manufarsa.
Kari akan haka: in munazara za a yi, in maslahar addini ake bukata; kar a barta ta isa kunnuwan gama-garin mutane, domin rawar da mukabalar da Sheikh Idris Abdu al-Aziz ya yi, tare kiyayewarsa ta taka rawar gani wajen kara fitowa da Muhammad Yusuf a matsayin wanda zai iya tunkarar manyan malamai kamar irinsa. Balle wacce ya yi da Dr. Isa Ali Pantami; ta fi shahara, su ma kansu sun fi jin dadinta, a samakakon shahararsa ya sa ta yi nisan kwana, kuma dalibai yan boko jahilan addini da yawansu sun zama yan ba boko.
Shi ya sa ba kowane mai haushi ba ne ahl al-Sunnah suke daga kai domin kallonsa, haka kuma bai haka yi masa raddi ba.
Watakila abin da zan kawo na maganganun malamai ya zama tuke ga yan uwana dalibai da ba su rigaya sun fada wannan tafarki da ambatonsa ya gabata ba.
al-Asbahaanee (R. A) ya ce:
"ﻗﺎﻝَ ﻋﻠﻤﺎﺀ ُ ﺍﻟﺴﻠﻒ : ﻣﺎ ﻭﺟﺪﻧﺎ ﺃﺣﺪﺍً ﻣﻦ
ﺍﻟﻤﺘﻜﻠﻤﻴﻦ ﻓﻲ ﻣﺎﺿﻲ ﺍﻷﺯﻣﺎﻥ ﺇﻟﻰ ﻳﻮﻣﻨﺎ ﻫﺬﺍ ﺭَﺟَﻊَ ﺇﻟﻰ ﻗﻮﻝ ﺧﺼﻤﻪ , ﻭﻻ ﺍﻧﺘﻘَﻞَ ﻋﻦ
ﻣﺬﻫﺒﻪ ﺇﻟﻰ ﻣﺬﻫﺐ ﻣُﻨﺎﻇﺮﻩ , ﻓﺪﻝَّ ﺫﻟﻚ ﺃﻧﻬﻢ ﺍﺷﺘﻐﻠﻮﺍ ﺑﻤﺎ ﺗﺮﻛﻪ ﺧﻴﺮٌ ﻣﻦ ﺍﻻﺷﺘﻐﺎﻝ ﺑﻪ"
"Malaman (daga) Salaf sun ce: ba mu samu (mutun) daya daga cikin ma'abota magana tun zamunan da suka shude zuwa yau dinmu nan da ya dawo zuwa ga maganar abin gogawarsa ba, ko ya yi kaura daga tafarkinsa zuwa na abokin tattaunawarsa, haka sai ya nuna cewa (ashe) sun shagalta gabarin abin da barinsa ya fi alheri sama da shagaltuwa da shi."(12)
Idan malami ya karkace gabarin turba aka yi kokarin dawo da shi ya subuce, sai an yi da kyar ba a samo shi kusa da shi'ah ba, koda kuwa a baya ya kasance mafi martani gare su!
Sheikh Adnan Ar'oor lokacin da ya tare gidajen Talabijin domin tattaunawa da yan shi'ah malamai da dama sun yi kokarin dawo da shi kan turba, sai ya kaikashe, har ya fara samun shakku akan wasu abubuwan da suke alaka da akidar sunnah, a wani lokaci ma akan iya cin zarafin wani sahabi a gabansa ba yadda ya iya, hakan har ya zamanto, ba wani bakon al'amari ne a wajensa ba, ya ci gaba da sharakawa har mafi girman fitina ta zo ta yayibe shi a sahun farko: fitinar khawarijanci akanta ya kare al'amarinsa: bayan tsawon lokaci akan mafaranta.
Shi ne ma'abocin shirin nan wanda ya yi sanadiyyar hallakar miliyoyin mutane: "مع سوريا حتي النصر - Tare da Syria har sai an cimma nasara" a karkashin wannan shiri ne ya wautar da fatawowin malamai akan haramcin fito-na-fito da gwamnati, ya ingiza jahilan matasa tare da taimakawar mai fatawar Ikhwan na Dr. al-Qardawee, da kuma Dr al-Aréfee mai fatawar auren jihaadi (نكاح الجهاد) wanda ya yi daidai da auren mut'ah (نكاح المتعة) wanda malaman musulunci sun yi ijmaa'i akan haramcinsa.
Mai yiwuwa wani ya ce, 'mun ji an ce: su al-Imaam Shaafi'i sun munazara,' amsa ita ce: sun yi amma da irin tsarin da suka yi ka ke yi?
Irin mutanen da suke saurararsu irin su ne a gabanku?
Dalilan da suka ingiza ka kana ga sun yi daidai da nasu?!
A karshe, mai yiwuwa wannan magana mai zuwa ta Shi al-Imaam al-Shaafi'in ta zama waraka ga masu irin wannan ciwo, ya ce:
"ﻣﺎ ﻧﺎﻇﺮﺕ ﺃﺣﺪﺍً ﻋﻠﻤﺖ ﺃﻧﻪ ﻣﻘﻴﻢٌ ﻋﻠﻰ ﺑﺪﻋﺔ "
"Ban taba munazartar wani mutun da na san tsayayye (taurararre) ne akan bidi'arsa" (13)
Amma wadanda suka munazarci Abdu al-Jabbar ba su san taurararre ba ne akan bidi'arsa, shi din wanda ya bata addininsa da mutuncinsa, don haka zai iya cin mutuncin wanda ya ga dama cikin bayin Allah na gari kamar yadda ya yi da Mu'awiyah (R. A)?!
A karshe, abin da manhajin ahl al-Sunnah ya fada dangane da yan bidi'ah akwai:
-Ukuba ga yan bidi'ah wanda wannan a hanun shugaba ya ke, Kamar yadda Umar (R. A) ya yi da Ibn 'Isl: ya yi ta magana akan mutshaabib, ya yin da lamarinsa ya isa when Ameer al-Mu'umineen ya bulale shi sa'annan ya sa aka kaurace masa na shekara domin a fahimci gaskiyar tubarsa.
-Ba a yabon dan bidi'ah saboda dan kunama ce da ba abin fahari ba!
-Ba a basu kariya, ba a kare littattafansu balle karantawa sai ga mai nufin martani.
Abubuwan suna da yawa, zan takaita akan wannan.
Allah sa mu wanye lafiya!
Tushen Bincike:
1- Majmu'al-Fataawah, Taimiyyah I. (2/132)
2- Salih al-Bukharee, Muslim. (59)
3- al-Qur'an al-Kareem, S. Noor. (63)
4- adhwaa' al-Bayan, al-Shanqeetee M.A. Suurah al-Noor (T)
5- al-Tahdheer Wa al-Tabyeen, 'Iid Abu Sa'uud K. (52)
6- al-Qur'an, S. al-Maa'idah. (2)
7- fawzan. co. uk
8- 4salaf. com
9- Salih Muslim, Muslim I. (49)
10- sharh al-Riyadh, al -Arba'in, Uthaimeen M. (5)
11- Ya Gabata A Na Biyar (5)
12- Lum'ah, and Others.
13- sharh Usuul al-'Itiqaad, al-Laalika'i I.
14- al-Aghaanee, al-Asbahaanee, A.
15- Min Kalaam al-Shaafi'i, I. (12)
No comments:
Post a Comment