Ko shakka babu Salafawa sun barranta da abin da ka danganta su da shi na:
1. Zurfafawa: Saboda sun fi kowa ƙoƙarin yaƙar zurfafawa a bisa Tafarkin Annabta. Martaninsu ga ƙungiyoyin zurfafawa da zafin kai a faɗin duniya samamme ne, kuma sananne, kamar martaninsu ga Ikhwan da Sururiyyah, da sauran ƙungigiyoyin da suka reshenta a kansu, kamar: al-Qa'idah, Taliban, da sauransu.
Kuma babu laifi na bijiro da wasu tambayoyi:
I. Su wane ne sanadin ingiza matasa kan tituna domin fito-na-fito da shugabanninsu, ba su ya cancanta a danganta su da zurfafawa ko zafin kai, amma menene laifin waɗanda suka yi musu nasiha, suka tsoratar da su gabarin saɓa wa Shari'ah?!
II. Su wane ne suke tsigale shugabanni a wuraren karatunsu da kan minbarorinsu, ba ire-irensu ba ne ya suka haifar da fitinar kangara da ake fama da ita?!
III. Su wane ne suka ƙarfafa lamarin magana a cikin addini da ra'ayi, kuma suka dage wajen raba alaƙar mutane da magabata na kwarai da waɗanda suke kan tafarkinsu, musamman a ɓangaren aƙida da manhaji?
2. Cire Mutane daga Sunnah ko shigarwa: Shi ma wannan ba aikin Salafawa ba ne, bal ma'abota tsantsani ne dangane da haka; abin da suka sani shi ne: tabbatar da abin da ya tabbata bisa ingantaccen dalili, da kore saɓaninsa, kuma ba fatansu kowa ya zama halakakke ba, kamar yadda galibin ƙungiyoyin da suke jingina kansu da sunnah suke yi a wannan lokaci, a nan Nigeria ko Niger.
3. Sheikh Dr. Aman al-Jami (Allah ya jiƙansa) sanannen malami ne mai tsaftacciyar aƙida da ingantaccen tafarki a wajen Malamansa, kamar: Sheikh Muhammad Ibn Ibrahim Ali Sheikh, Sheikh Abdulaziz Ibn Baz, da sauransu.
Ƙari a kan haka, duk abin da Sururiyyun suke tuhumarsa da shi na martani ga wasu ƴan zafin kai da kuka dauka a matsayin malamai, lallai Sheikh Ibn Baz ya kamata ku tuhuma, saboda shi da ƴan uwansa malamai suka fada fatawar halaccin shigowar Sojin America Saudi Arabia domin tunkuɗe kwararar Saddam Hussein cikinta, shi kuma Sheikh Aman al-Jami ya bada kariya ga fatawarsu wacce take ɗore kan ilmi, da hikima, da hangen nesa.
4. Sheikh Rabee (H. A) ɗalibin Sheikh Aman ne, kamar yadda kasance ɗalibin manyan malaman zamaninsa, kamar: Sheikh Ibn Baz, da Sheikh al-Albani da suransu, kuma ya samu yabon alheri daga wajensu, bal ma sun ƙarfafe shi dangane da martanoninsa ga ƴan sururiyyah, hasali ma Sheikh Ibn Baz ya faɗa masa: Ko ni na yi ba daidai ba ka yi min martani.
Ƙari a kan haka, an taba tambayar Sheikh Uthaimin a kan jagoran Qutbiyyah Sayyid Qutb ko littattafansa, sai ya yi nuni zuwa ga rubuce-rubucen Sheikh Rabee (H. A) a kansa ko kansu.
5. In har wani tsohon ɗalibin Jami'ar Musulunci Ta Madinah zai danganta tsofin malaman malansa da fitina, alhali sun barranta daga gare ta, kuma sun kai mataki na ƙarshe a ɓangaren karantarwa, da bincike, da riƙe matsayi, ko shakka babu shi ya faɗa cikin fitina.
Ƙari a kan haka: Idan danganta malaman da suka samu mafi darajar shaida a wajen malaman zamaninsu da fitina bai zama abin mamaki ba, bai kamata a ce danganta malaman da suka samu kushe, tsigalewa, da tsoratarwa daga malamansu ya zama abin mamaki ba. Wannan shi ne misalin waɗannan malamai biyu: Sheikh Aman al-Jami da Sheikh Rabee al-Madkhali da sauran Malaman Sururiyyah, kama daga kan Muhammad Surur Zain al-Abidin zuwa kan Dr. Salman al-Audah.
6. Kamar yadda ka ce: kun barranta daga Salafawa, lallai Salafawa ma sun barranta da Sururiyyah da ƴan tsakinta, kuma ba za su kasance a cikin ƙasƙanci ko faɗuwar gaba ba dangane da haka.
7. Wannan tunatarwa ce, kuma na san Mal. Ahmad Tijjani Yusuf ma yana wajen aka yi, zai iya tuna maka idan ka manta.
Allah ya shiryar da mu zuwa ga gaskiya da aiki da ita.
©Ibrahim Lawal Soro
12. 03. 2022 CE.
No comments:
Post a Comment