Tare da yawan
lik'e-lik'enka akan ture-turen da na ke yi, musamman kafin ka d'eb'e tsammani
ga barina ban tab'a yi maka martani ba!
Saboda dalilai masu yawa, kamar:
-Kasancewar ba na iya fahimtar abin da ka ke rubutawa, saboda yawaita had'el a wajen rabel da rabel a wajen had'el, hakan ya bayu ga nisansar abin da yarintarka ta rubuta maka.
-Bai kamata na b'ata lokacina domin ganowa abin da ka rubuta ba, daga bisani na ce zan maka martani, ka ga b'ata lokaci sau biyu kenan!
-Abin da ka ke lik'awa bisa ga yadda na fahimci wani sashinsa ba zai wuce talk'inin wannan iblishin ba: Umar Mansur mai gidan Ikhwaqutubawan da suka mamale galibin daliban Najeriya anan Egypt; kar Allah ya k'addara amma idan yanayin ya ci gaba a irin wannan salo da wasu mabarnata, maruwanta, da d'aid'aita manhajin magabata na kwarai ya ci gaba, tabbas za a ci gaba da yaye rikitattun malamai masu rikitarwa.
Ba zai b'aci ba idan na buga misali da babban mai gidanka a lokacin da ya ke gani -bisa jahilci da rashin wayewa da sunan wayewa- ya kamata mutanen arewacin Najeriya su fito zanga-zanga domin nuna fushin su akan turen Amurka na sojoji.
Madogararsa ita ce: tun da masu 'tereren a kawo mana 'ya'yanmu gida' ya samu karb'uwa -tare da kaud'en bai san dalilan da ya sa ya samu k'arb'uwa ba.
Irin wannan mai k'ona zuciya ce; ba shi kadai ba, akwai ire-irensa da suke ganin hanyar b'ata mafita ce.
A Jan/2014 muna k'ok'arin shiga jarabawa, mun zauna kusa da wasu tarin taron dalibai Misirawa, daga bisani suka b'uge ta zanga-zanga sai na shawarce shi da gusawa, amma bai mik'a wa batun nawa wata dama ta tasiri a zuciyarsa ba balle ta ingiza gabb'ansa zuwa ga matsawa tare da ni, bal ya biyo ni ma da wata kalma maras dad'in ji da maimaitawa: 'ya yi daidai, kuma ba na fatan su daina,' ya fad'a ko a jikinsa, amma tare da haka sai da na aika masa tambaya, 'yanzu kana ga za ka iya k'iran mutane a fito zanga-zanga kamar yadda malaman Ikhwan suke yi? ' 'Eh mana, sai dai ba yi zalunci ba' ya amsa da karfafawa.
Ban gushe ba sai da na k'ara masa da cewa, 'lallai za a yi mabarnacin malami a Burkina-Faso in har wannan shi ne abin da za ka kai musu: abin da ka jida akan titi, watsarwar 'yan tasha, da turawan hallakarwa.
Ba ya daga cikin manhajin magabata na kwarai: bada kariya ga 'yan bidi'ah, wannan shi ne aikin 'yan uwanka, akansa suke soyayya da k'iyayya.
An tambayi al-Allaamah Bin Baz akan wad'anda suke kare 'yan bidi'ah, suke yabonsu, da nema musu mafita, shin za a had'a shi da su?!
Sai ya amsa da fad'insa:
"ﻧﻌﻢ
ﻣﺎﻓﻴﻪ ﺷﻚ , ﻣﻦ ﺃﺛﻨﻰ ﻋﻠﻴﻬﻢ ﻭﻣﺪﺣﻬﻢ ﻫﻮ ﺩﺍﻉ ﻟﻬﻢ , ﻳﺪﻋﻮ
ﻟﻬﻢ , ﻫﺬﺍ ﻣﻦ ﺩﻋﺎﺗﻬﻢ , ﻧﺴﺄﻝ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻌﺎﻓﻴﻪ"
"Na'am, ba bu shakka akan haka, duk wanda ya yabe su ko ya kwad'a su, (to) shi mai k'ira ne zuwa gare su, yana musu k'ira (da'awah), wannan (ma) yana daga cikin masu da'awarsu, muna rok'on Allah (zaman) lafiya."
A tak'aice zan bi wannan sak'o naka domin fitowa da abin da ya ke cikinsa, abin da ya gabata ka d'auke shi a matsayin TAK'AITACCIYAR GABATARWA.
Al-amin Adam ya ce:
"Assalamu alaikum nayi wannan rubutu ne sboda
yanuwa da suke nijeriya kada a dinga rudarsu da
karairayi da sunan salafanci"
Wa alaikum al-Salam warahmah
Wannan wasik'ar taka ba ta shanshani kamshin 'yan uwantaka ba, saboda abubuwa biyu da ta kunsa:
-Kore mutane daga alheri: wannan kuma ya bayyana k'arara a k'ark'ashin tsoratar da su da ka yi ga barin Salafiyyah, wannan aika-aika kaima gani ka yi na gabanka suna yi, don haka ban ga bak'on abu a cikinsa ba; jifar da ka yi da wuya ya samu wad'annan 'yan uwa da suke k'ok'arin fahimtar da'awar salafiyyah.
-Tura su zuwa ga sharri: wannan sak'on naka inda ka aika musu kana mai bayyana musu halin k'ungiyar Ikhwanul Muslimin (akan) cewa ta ta'addanci ce, had'arinsu ya fi na Boko-Haram, bal (ma) su ne iyayen gidansu na asali, inda ka yi haka, 'yan uwanmu sun fahimci tsinatar aikinsu, da ka samu lada, da ka toshe wata kafa da yawancin mutanen Najeriya suka afkawa mutuncin wasunsu ta hanyarta: la'antar hukumar Egypt bisa jahiltar abin da ya ke faruwa.
K'ari akan haka, d'ab'i'ar da suka tsinci kansu ce ta ke b'uk'atar tankad'e da rairaya: sauk'in sakin baki a wajen masu k'arajin kishin musulunci a fili ya ke, musamman wad'anda suke alak'anta kansu da Sunnah. Hakan kuma yana da sila da tasirin kwashe-kwashen wasu malamai da suke kwasa daga wajensu, musamman dangane da halin da duniya ta ke ciki a yau.
Wanda ya jahilci ko jahiltar da kansa jiya, ina zai iya fassara a yau d'inta?!
Subhanal Lah! Lamarin ya kai ga kafirtarwar da fasik'antarwa da wasu suka d'auka a matsayin mafita dangane da lamarin, ka ga wanda ya yi d'uren irin wad'annan masifofi ga jahilan mabiyansa ya cancanci azabtarwa bisa ga laifinsa da bankad'e halinsa.
Bugu da k'ari, in magana ta masu adalci za ka yi, masu nasiha da gaske, da ajiye abubuwa a gurabensu, sai ka kawo k'arerayin da aka yi, daga bisani ka ruguje su da gaskiyar da ta ke wajenka.
Wannan shi ne salon da ake bi wajen d'aurewar adalci a cikin al'umma.
Al-Amin ya ce:
"shin irin wannan
zagin da sokiburutsu da wadanda kuke cewa
malamai suke fada shine salafanci suzo suna
fadawa masu kokari wadanda wasu ma acikinsu
ana musu fatan aljannah amma kun shagala da
zaginsu ku bayan baku gabatarwa da addinin
komai ba."
Maganarka tana buk'atar abubuwa guda biyu wad'anda da su ne za a sallama mata:
-Na farko: -kamar yadda na fad'a a sama- guraben zagin ya kamata ka kawo domin wad'anda ka rubuta wasik'ar taka zuwa garesu su samu cikakken aminci dangane da kalmominka.
Na biyu: bayan ka kawo sai a duba shin haka zagi ya ke ko kuma kai ne ka k'iara shi saboda korel?! In zagi ne, magabata na kwarai sun zagi 'yan bidi'ah ko ba su zaga ba?! In kuma tsauri ne ba wanda ya taba yin wanda ya fi tsauri daga cikin magabata na kwarai ga 'yan bidi'ah da son zuciya?! Ko kuma ka jefo waccar kalmar taka ce domin ka kunna wutar neman tausasawa daga wad'anda ba su san abin da su ke yi ba kamar waccar makwabciyar taka: Fateema mai kokarin jefa kanta tafarkin 'yan ruwantarwa?!
Ka k'ara akan haka: abin da karantarwar sunnah ta d'oru akansa shi ne: fatan al-Jannah ga kowane musulmi tare da la'akari da aiyukansa, kana ana tsorata masa wuta saboda sab'onsa, in kuma ya mutu yana cike da sab'on da bai tuba gare shi ba, ba a masa masauk'i a wuta ba; yana k'ark'ashin mashi'ar Allah: in ya so ya gafarta masa da falalarsa, ko ya azabtar da shi da adalcinsa bisa ga abin da ya ke kai na sab'o. A sakamakon wannan kowane musulmi wanda ake tsammanta masa al-Jannah ce, ba wasu ba, in kuma fuskar bayyana cancantar su ce akan wasu, bayan abin da ya ke fayyace dangane da su na bidi'ah to wannan kuskure ne, wuce gona da iri ne, kodayake wannan bak'on abu ba ne a wajen Ikhwaniyawa Khawarijawa.
Lamarin kuma a fili ya ke: duk k'ok'arin da mutun ya yi a tafarkin Allah in ya zo da dalilan rushe shi ba abin da zai hana rushuwarsa.
Mai yiwuwa ne yau kana musulmi gobe ka zo da abin da zai fitar da kai daga cikinsa fitarwa, haka ita ma sunnah daidai-wa-daida.
Ka ce:
" waye raslan a duniyar ilimi mai yayiwa
daa war sunnah har da zaa zo ana kamba mashi
irin abubuwan da yake fada akan mimbari jahilai
ma ba zasu fada ba"
al-Allaamah Raslan (H. A) yana daga cikin wad'anda suka shahara da hidima wa Sunnah a wannan zamani; lamarinsa bai b'uya ba a wajen wanda ya san abin da ya ke gudana a da'irar duniyar Sunnah, ya toshe kafar da ba wani malamin Sunnah da ya toshe a wannan k'asa, musamman bayan Rasuwar sheikh Mahmud Shaakir (R. A).
Kodayake daga cikin malamai akwai wad'anda ba su buk'atar taskiyar wani kafin a shaida kafuwarsu, adalarsu, da tsantsaninsu wanda ina kyautata zaton al-Allaamah Raslan ya kai wannan mataki, tare da haka yana da taskiyyar malamai sama da talatin (30) daga Hijaaz, Yemen, Misr, da Shaam, zan yi amfani da wannan dama na gutsuro sashin wacce al-Sheikh Dr. Sa'ad al-Hasein daga Hijaaz ya yi masa:
"الشيخ رسلان يذكرني احمد بن حنبل . . . "
"Sheikh Raslan yana tuna min (Imam) Ahmad d'an Hambal (R. A)"
Shehin malamin ya fad'i wannan magana ce la'akari da ya yi akan irin wahalhalun da wad'annan mabarnata su ke ba bashi: tare da tarin dalibai da ya ke da su, da shagalta wajen karantarwa, ya kuma kebance wani sashi na lokacinsa domin martani da yaye shubuhohin khawarijawan zamani (ikhwan), bai taba ja baya ba, tare da gargadi da alk'awuran da suka rink'a aika masa.
Ya d'auki wannan nauyi gaba d'ayansa a wuyansa: bayyana b'atar mab'arnatan da suke jingina kansu da Salafiyyah tare da nisansu ga barinta da ya kai nisan sammai da k'assai.
Al-amin ya ce:
"sati biyu da suka wuce ya
hau yana ta karairayi Allah ya kunyatar da shi a
idon duniya sai gashi har wasu a najeriya sunzo
suna ruduwa da shi kuma ba kowa bane a
duniyar ililmi ba."
Dangane da maganarka ta sama in kana zancen 'zanga-zangar samarin musulunci 'yar makami' ne ba shi ya yi k'ira a fito ba -Allah ya tsare shi daga khawarijanci- shi ma kamar waninsa ne; sanarwar ce ta iske shi, kamar yadda ma'abotanta suka yad'a ta a kafafen sadarwa, sak'on nasu kuma ya iske duniya gaba dayanta, na yi rubutu akan wannan batu ana washe-garin aika-aikar, wato 27/Nov/2014 kenan, in za ka iya rushe abin da na kawo da dalilai ka duba shafina za ka tsince ta.
Bugu da k'ari, aikin da al-Allaamah ya ke yi a matsayinsa na malami mai nasiha don Allah, shi ya sa a ranar ya ce: mutane su gujewa masifa, su nisanci ma'abotanta, da tsare kawunansu da iyayensu ga barin ruftawa cikinta tare da shagwab'abb'u, 'yan ta'adda, da tada zaune tsaye. Sa'annan ya k'ara fitowa da tsare-tsaren Ikhwan na tada k'ayar baya a k'asarnan tare da 'yan uwansu ISIS.
Duk wanda ya ke wannan dandali matukar yana abota da wani Bamisre zai ga batun a shafinsa, yana mai goyon baya ko sabaninsa, hatta gasasshen Ikhwaqutubin nan Umar Mansur na ga ya yi 'Like' wannan batu, ta wannan b'angaren kenan.
Ta b'angare guda kuma hukumar k'asar nan ta shirya tsaf domin tunkarar su: kungiyar Ikhwan din da 'yar tata ISIS da suka ce ta faso Egypt, har ma ta iso al-Ahraam na al-Jeezah.
Anan menene laifin al-Allaamah Raslaan don sun k'i fitowa?
Kuma k'in fitowar tasu ta hana hukuma cafke wad'anda suke da hanu dumu-dumu a shirye-shiryen nasu?!
A'a, ko kad'an, saboda a ranar ina gida a zaune, ba na fita sai sallah da wasu buk'atun dole, kamar fansar abin ci da sha, na ziyarci makwabcina domin ganin halin da garin ya ke ciki, anan ne na ga irin tsarin da hukumar ta yi na tunkarar ta'addanci da 'ya'yansa, tsarin da koda rabi hukumar k'asar mu ta yi da tunin ta rushe wad'ancan jikanun Hassan al-Bannaa da Sayyid Qutb tunin an burne su a mak'abartar tarihi, anan ne na ga d'imbin mutanen da aka kama a al-Qaahirah, al-Iskandariyyah, da sauransu.
Bisa ga wannan, kai ne mak'aryaci, mayaudarin da ke son tunzura wasunsa kogon koyi da ire-irensa a wannan fannin k'age da fagen tadlisanci.
In kuma na baka misali ba zai b'aci ba, k'ila lamarin ya k'ara bayyana a wajen waninka:
Akwai wani shafi a wannan dandali da jiga-jigan Ikhwaniyawa suke shan manhajin Khawarijancin da ya narke a manhajin Ikhwaniyanci, kamar wannan ibishi Sulaiman Mahmoud Abdullah da sauran mutane goma sha shida (16), sunan wannan sha fi kuma 'الازهر اليوم' yana daga cikin shafukan da suka sanar da waccar la'ananniyar 'Thaurah' da ambatonta ya gabata.
In tak'aice maka zance, dabi'ar k'arya wa malamai da zaginsu ta ku ce ba ta waninku ba, ka tambayi ibishin nan Nura Musa, da sauransu.
Ba ka hak'ura ba ka k'ara da cewa:
"sannan makiya Allah shi da ire-
irensa sukewa aiki.A tsakninsu ma masu irin
daawar tasa bidiartar da juna suke."
Mak'iyin Allah (S. W. T) da manzonsa (S. A. W) shi ya ke k'ok'arin dushashe hasken musulunci, musamman da'awar sunnah tare da wautar da ita.
Wannan siffa kuma ta k'are a gindin Ikhwaniyawa: sun datse wa mutane hanyar gaskiya sun tura su halakar da duniyarsu da lahirarsu.
Yana da kyau ka sani, Salafiyyah ba Ikhwaniya ba ce -wannan shi ne abin da Maha'incin nan Nura Musa ya kasa fahimta, tare da tsantsar ji da kansa, ina ga kai d'an tsakonsu, tare da kamanceceniyarku ta fuskar rashin iya rubutun Hausa, shi ya sa ma sharrinku ya k'aranta- ma'abotanta suna martani ga duk wanda ya ratso cikinta da wata bidi'ah, nan take su ke mayar masa kayansa, duk irin hidimta mata da ya yi ta hanyar da ta dace da matsayinsa, sab'anin Ikhwanu(n) da Mu'assasinta al-Banna ya k'irk'ira mata wata ka'ida da ta mamaye mutane gaba d'ayansu tare da bambancin ak'idunsu, bal ta shigo hatta da kafirai cikinta, wannan shu'umar ka'idar ita ce:
"ﻧﺘﻌﺎﻭﻥ ﻓﻴﻤﺎ ﺍﺗﻔﻘﻨﺎ ﻋﻠﻴﻪ، ﻭﻳﻌﺬﺭ ﺑﻌﻀﻨﺎ ﺑﻌﻀﺎ ﻓﻴﻤﺎ
ﺍﺧﺘﻠﻔﻨﺎ ﻓﻴﻪ "
"Za mu rink'a taimakekkeniya akan abin da muka yi gamonkatar akansa, sashi kuma ya rink'a uzuri wa sashi akan abin da muka saba akansa"
Wannan ita ce shaidaniyar k'a'idar, akanta babban mai fatawarku ya ke gudana: Yusuf al-Qardaawee ya b'arnatar da karantarwar Sunnah -Allah ya biya shi da abin da ya yi.
A k'ark'ashin ta ne kuma Muhammad al-Hassan ya ke k'iran Sufaye, Shi'ah, da sauran jiga-jigan 'yan bidi'ah duk ya k'ira su da 'yan uwansa, a lokacin da tsohon Shugaban k'asar Iran Mahmud al-Abbas ya zo k'asar nan a mulkin Ikhwan, sai Muhammad al-Hassan a wajen tarb'arsa a bakin Ikhwan ya ce: 'yan uwanmu shi'ah, sab'anin da ya ke tsakaninmu na tunani ne (ya na nufin ba na ak'ida), domin neman gindin zama da tsananin kwad'ayin 'Markusancin Leniniyanci' (Marxist-Leninism) wanda ya d'and'ana daga wajen Sayyid Qutb.
A tak'aice, Salafiyyah suna martani ga 'yan uwansu, balle wad'ansunsu.
Ba kamar yadda ku ke surantawa ba!
Ka ce a kammalawarka:
"to kira ga
dalibai ina mai basu shawara da idan basu sani
bane to tun wuri gwara suje su nemi malamai na
gari idan kuwa sun sani ina mai basu shawara da
suji tsoron Allah kada a rude su da wadannan
gurbataccen manhajin wanda su kansu zagin
kansu sukeyi basu ma san manhajin salaf assalih
ba."
Nima ina k'ira kamar yadda ka yi ga 'yan uwa dalibai, musamman wad'anda suke Najeriya kuma ba sa bibiyar abin da ya ke yawo a fagen fahimtar masu da'awah da su rik'e hanyar bayin Allah, wad'anda suka shahara da ilmi da amana, ba 'yan caji da tunzurawa ba!
K'ila malaman da ke maganarsu ba su wuce wad'annan 'yan ruwantarwar ba, masu ingiza mutane tafarkin khuruuji ta hanyar zaburarwa da kwad'aitar da zuciyarsu.
k'ari akan haka, wad'annan da ku ke fushi akansu -tare da tarin aika-aikarsu ga tafarkin Sunnah-ba kowanku ya had'u da su ba, in kuma ta kasance ba ta wuce sau d'aya ko biyu ba, saboda sun guji masallatai sun koma 'dak'unan shirye-shirye' (Studios) na gidajen talabijin da sauransu.
Alheran da malamai suke yad'awa ta hanyar mu'amalantar mutane ba sa yi, ba sa kusantar gama-garin daliban da ya kamata a ce sun tsotsa daga ilminsu, kad'ai yardaddun dalibansu ne suka san mak'wancinsu sai wakilan tashoshin da suke yad'a shirye-shiryensu.
Akan jifarka garemu na rashin fahimtar manhajin salafiyyah, numfasanmu sun yi shaida akan haka.
Masu bibiyar al'amura sun fahimci wad'anda al'umma ta ke amfana da su amfana ta hakika, da wad'anda al'umma ta ke rushewa da su rushewa a fili.
Kamar yadda ka sani: a yanzu mutanen Najeriya sun gama fahimtar halin Boko-Haram da motsinsu, haka mutanen k'asar nan suka fahimci halin Ikhwaan al-Muslimeen, sai 'ya'yan kungiyarsu da wad'anda son zuciya ya mamaye su.
Ina rok'on Allah ya yanke bayansu.
A karshe, ya zama wajibi ga kowane mai danganta kansa zuwa ga Sunnah ya san manhajin Sunnah, saboda samun matsala akansa ya kan taba ak'ida kamar yadda ya zamanto samun matsala a ak'ida samunta ce a manhaji, hakan kuma ya kasance ne saboda lazimin da ya ke tsakaninsu, ta yadda wani bai isa ya ce zai raba su ya samu zaman lafiya ba, kamar ya ce: "zan rik'e ak'idar sunnah, amma zan d'auki manhajin khawaarij ko mu'utazilah dangane da umarni da kyakkyawan aiki da hani ga barin munmunan aiki, ko zan rik'e manhajin annabta akan ibada da akidar sufaye akanta."
Irin wannan tsari b'atacce ne, kuma ba zai amfanar da shi da komai ba, saboda samun karkata akan d'aya yana shafar d'an uwansa.
Wannan batu mutane masu dama daga cikin wad'anda suke danganta kansu da Sunnah sun b'ace ga barinsa.
Akan wannan batu al-Allaamah al-Fauzaan ya ce:
"ﻭﻻ ﻳﻤﻜﻦ ﺃﺗﺒﺎﻋﻬﻢ ﺑﺈﺣﺴﺎﻥ ﺇﻻ ﺑﺘﻌﻠﻢ
ﻣﺬﻫﺒﻬﻢ ﻭﻣﻨﻬﺠﻬﻢ ﻭﻣﺎ ﻳﺴﺮﻭﻥ ﻋﻠﻴﻪ، ﻭﺃﻣﺎ ﻣﺠﺮﺩ
ﺍﻻﻧﺘﺴﺎﺏ ﺇﻟﻰ ﺍﻟﺴﻠﻒ ﻭﺍﻟﺴﻠﻔﻴﺔ ﻣﻦ ﻏﻴﺮ ﻣﻌﺮﻓﺔ ﺑﻬﺎ
ﻭﺑﻤﻨﻬﺠﻬﺎ ﻓﻬﺬﺍ ﻻ ﻳﺪﺭﻱ ﺷﻴﺌﺎ؛ ﺑﻞ ﻗﺪ ﻳﻀﺮ، ﻻﺑﺪ
ﻣﻦ ﻣﻌﺮﻓﺔ ﻣﻨﻬﺞ ﺍﻟﺴﻠﻒ ﺍﻟﺼﺎﻟﺢ . . "
"Ba ya yiwuwa binsu (magabata na kwarai) sai ta hanyar karantar mazhabarsu, manhajinsu, da abin da suke gudana akansa, amma tsantsar ik'irarin danganta da Salaf da Salafiyyah ba tare da saninta da manhajinta ba, (to) wannan bai san komai ba, zai iya cutarwa ma, ba bu makawa a san manhajin magabata na kwarai."
Ya k'ara da cewa:
" ﻭَﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ
ﺍﺗَّﺒَﻌُﻮﻫُﻢْ ﺑِﺈِﺣْﺴَﺎﻥٍ) ﺗﺸﺪﺩ ﺍﻟﺤﺎﻟﺔ ﺇﻟي ﻣﻌﺮﻓﺔ ﻣﻨﻬﺞ
ﺍﻟﺴﻠﻒ ﺍﻟﺼﺎﻟﺢ ﻟﻠﺘﻤﺴﻚ ﺑﻪ ﻷﻧﻪ ﻃﺮﻳﻖ ﺍﻟﻨﺠﺎﺓ ﻛﻠﻬﺎ
ﻓﻲ ﺍﻟﻨﺎﺭ ﺇﻻ ﻭﺍﺣﺪﺓ ﻭﻫﻲ ﺍﻟﻔﺮﻗﺔ ﺍﻟﻨﺎﺟﻴﺔ ﻭﻫﻢ
ﺃﻫﻞ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﻭﺍﻟﺠﻤﺎﻋﺔ، ﺇﻻ ﻭﺍﺣﺪﺓ ﻭﻫﻲ ﺍﻟﺘﻲ ﺇﺫﺍ
ﺍﺧﺘﻠﻒ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻭﻛﺜﺮﺕ ﺍﻟﻤﺬﺍﻫﺐ ﻭﻛﺜﺮﺕ ﺍﻟﻄﺮﺍﺋﻖ
ﻭﺍﻟﻔﺮﻕ ﻭﺍﻷﺣﺰﺍﺏ ﻫﻲ ﺍﻟﺘﻲ ﺗﻜﻮﻥ ﻋﻠﻰ ﻣﻨﻬﺞ
ﺍﻟﺴﻠﻒ ﺍﻟﺼﺎﻟﺢ ﺗﺘﻤﺴﻚ ﺑﻪ ﻭﺗﺼﺒﺮ ﻋﻠﻴﻪ ﺣﺘﻰ ﺗﻠﻘﻰ
ﺭﺑﻬﺎ ﺳﺒﺤﺎﻧﻪ ﻭﺗﻌﺎﻟﻰ"
"(Fadin Allah) "wad'anda suka biyo su da kyautatawa" tana tsananta halin buk'atuwa zuwa ga sanin manhajin magabata na kwarai domin rik'o da shi, saboda shi ne hanyar tsira, (saboda fad'in Manzon Allah) "dukkansu suna cikin wuta sai guda d'aya" ita ce jama'ar tsira: ahl al-Sunnah wa al-Jamaa'ah, 'sai guda d'aya(n nan) ita ce idan mutane suka yi sab'ani, mazhabobi suka yawaita, 'Darik'u suka hayayyafa, kuma jama'u da k'ungiyoyi suka yawaita, ita ce (kad'ai) ta ke kasancewa akan tafarkin magabata na kwarai, take rik'o da shi, take hakuri akansa har sai ta had'u da Ubangijinta tsarki ya tabbata gare shi ya d'aukaka. "
Anan sai mu yi wasu 'yan tambayoyi kamar haka:
-A wannan zamani da muke cikinsa, mabiyan tafarkin magabata na kwarai su wanene ba Salafawa ba?!
-Shin ba su ba ne a lokacin da Ikhwan ta ke son lankwame kowa suka k'ara rik'e ta tafarkinsu gamgam, saboda tsera wa fitinarsu?!
-Ba su ba ne suke yaye duk wani sharri da aka nufaci musulunci a game, da sunnah a keb'ance ba, ko Ikhwanu(n) da ta ke fatan shigowar ISIS k'asar nan ce?!
-Wa duniya ta ke kuka a sakamakon da'awarta, Salafiyyah ko Ikhwaniyyah?!
-Shin ba Ikhwaniyyah ba ce uwar ta'addancin zamani da ake jingina wa musulunci a game, da Sunnah a keb'e?!
Tambayoyin suna da yawa amma wad'annan su ne kad'an daga cikin wad'anda suka shafi wannan batu, ina rok'on Allah (S. W. T) ya maida b'atattu, zamammu, da masu kuskure kan tafarki.
Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabinmu Muhammad, iyalansa, sahabbansa, da wad'anda suka bi yo su da kyautatawa.
Ibrahim Lawal Soro
al-Azhar University, Cairo, Egypt
Faculty Of Shari'ah And Common Law
5/12/2014C.E.

No comments:
Post a Comment