1.1 Gabatarwa
Tun lokacin da bidi'ar farko ta bayyana: bidi'ar khawarij a shekarar (35) Hijrah,
daga nan Allah yake tsaida gwarzon da zai
nakasa kowa ce bidi'ah ta hanyar since mata zani a kasuwa, da bayyana karkatar ma'abotan ta, haka lamarin yake tun
bayan ya turo da cikamakin annabawa: Muhammad Bnu Abdillah (S.A.W) da
hasken muslunci wanda ya dushashe hasken shirka da kafirci.
Dangane da bidi'ar khawarij da shi'ah sai Allah ya tanada mata Khalifan
musulunci na hudu: Aliyu bnu Abi Talib, a tare dashi akwai:
Abdullah bnu Abbas da makamantansa da cikin sahabbai (R.A).
1.2 Manufofinsu
Khawarijawa da ƴan zanga-zanga sun yi tarayya akan manufofi daya, daga cikinsu akwai:
i. Sauke shugaba daga karagar mulki, ta hanyar fitowa a gare shi, da harshe a farkon lamari, kamar:
Zaginsa,
aibata shi da nuna wa gama-garin mutane gazawar sa
har wutar kiyayya ta kunnu tsakaninsa da wadanda Allah ya damka kiyonsu a hanunsa.
Sa'annan fitowa da makami a karshensa;
a yayin da suka ga rashin dacewarsa, ko kafircinsa -a tunaninsu.
Wannan kuma shi ya faru a lokacin khalifancin Uthman Bnu Affan,
bayan Abdullah Bnu Saba'i ya yada kiyayyarsa a zuciyar dake da ciwon jahilci,
da son barnata addini da duniya.
Ibnu Taimiyyah yace: "Ba wasu mutane da zasu gaza hakuri akan zaluncin shugaban su,
su yake shi,
face sharrin da zai biyo baya -bayan yakin- ya dara wanda suka kasa hakuri akan sa."
Allah jikan ka Shehun musulunci,
hakika mun ga haka, tun daga lokacin Khalifan Manzon Allah Uthmanu
Izuwa mai biye Masa Aliyu,
Mun karanta abinda ya faru da Hussaini Ibnu Aliyyi bni Abi Talib,
littattafan tahiri
sun yo mana guzurin abinda ya wakana a lokacin Hajjaaju bnu Yusuf.
A takaice shi muke gani a Afganistan, Iraq, Libya, Syria, Nigeria, da Misra.
ii. Bata addini da yi masa mummunan wakilci a idon makiyansa,
daga bisani kashe akidar wala'i da bara'i
ta yadda masu zanga-zangar a wasu lokuta suke haduwa da arna; tare da kiransu yan uwa da sauransu.
iii. Kawowa kafirci, bidi'a, da ilhadi da sunan shari'ah.
iv. Farauto da yancin kafirci, ridda,
barnata akida ta hanyar kirkirar wani kundi daya saba wa shari'ar muslunci.
v. Zake wa duniyanci da neman abinda nemansa ta irin wannan hanya kuskure ne,
ta yadda zai iya yiwuwa a rasa shi gaba daya, sa'annan da karuwar wani abinda ba'a san shi ba, kuma ba'a tsammanin sa ba.
vi. Yaduwar ta'addanci da barna aban kasa, kamar yadda muke gani a yanzu,
aminci ya karanta, rayuka sun mutu, kasa ta wargaje, kowa yana cikin wani maye sai wanda Allah ya tseratar.
Wani magabaci na kwarai yace:
" Sha'awa da son zuciya suna galaba akan hankali da bayani."
shi yasa a wannan al-amari wasu daga cikin masu hankali sha'awarsu da son zuciyarsu suka rinjayi hankalinsu da ilminsu,
suka kutsa tare da mabarnata, yan son barkewar addini da duniya, masu kaunar zuban jini da mutunci.
1.3 Matsayin Zanga-Zanga Da Khuruuji
Ba shakka akan bidi'ancin zanga-zanga da khuruuji,
ya ishe su abin kunya da ba wani mutumin kirki cikin wadanda suka gabata -sai wadanda kafarsu ta zame, suka yi nadama kafin rasuwarsu- da yayi zanga-zanga da khuruuji,
Shi yasa Abdullah Bnu Abbas yace wa khawarijawan da suka fito wa Aliyu Bnu Abi Talib:
'babu daya daga cikinsu a cikinku.'
Yana nufin sahabban Manzon Allah.
"Yan bidi'ah dukkansu khawarijawa ne, sun bambanta a suna, sun hadu a takobi."
Inji Ayyub as-sukhtiyani. Daya daga cikin wadanda suka shahara da son sunnah da taimakonta a lokacinsa.
Akwai sama da malamai hamsin a wannan zamani namu da suka yi fatawa da rashin halaccin zanga-zanga,
sun bayyana fasadi da take kawo wa addini da duniya,
har wani daga cikinsu yace,
'ita ce kanwa uwar gami na abinda yake faruwa na hallakar rayuka a kasashen musulmai, '
ya kara da fadin,
' asalinta ba addini bace, ba wani addini daya zo da ita, koyi ce da turawan yamma,
daga can wasu mabarnata suka yayubota,
suka kawo ta da sunan
hanyar karbar yanci,
hanyar fita daga kangi,
hanyar nuna fushi da fusata,
amma ba'a san ta a al-adar kowa ce kabila daga cikin kabilun larabawa ba, balle addininsu:
addinin musulunci wanda ya karantar da hakuri da zaman lafiya tare da shugaba.'
Daga cikin malaman an samu wanda yace,
' Duk wanda aka kashe a dandalin zanga-zanga yayi mutuwar jahiliyya, kuma jininsa yana kan malamin daya fito dashi da maganarsa, ko abokin daya jawo shi, ko matar data lallabe shi.'
Daga cikin Malaman da suka yi fatawa da haramcin zanga-zanga, sa'annan suka alakanta ta da khuruuji akwai:
1. Al-albani -Allah ya jikansa.
2. Ibn Baz -Allah jikansa.
3. Uthaimeen -Allah jikansa.
4. Muqbil -Allah jikansa.
5. Rabee -Allah kara masa lafiya.

1.4 Fuskar
Kamanceceniyarsu
Idan kasan ko su wanene khawarijawa, da siffarsu zaka gane manhajin ƴan zanga-zanga.
Wadannan sune siffofin da suka yi tarayya:
1. Khawarijawa suna tawilin ayoyi da hadisai yadda suke so, haka ƴan zanga-zanga.
Misali: 'mafi girman jihadi itace kalmar gaskiya a wajen shugaba ja'iri.'
A karkashin wannan hadisi sai ka ji suna ce, 'ya halatta a fito a fada masa gaskiya a gaban kowa, ya halatta a yayata shi a gidajen telebishin da mujallu.'
Alhali 'a wajensa' aka ce, ba akan minbari ba, balle kan tituna,
jikin katangu da tebura.

1. A wajensa' ana nufin a kadaita dashi, ba cikin jama'a ba,
saboda kar girman kai ya hana shi karbar gaskiya, wacce itace tsirarsa,
hasali duk mai nasiha tsirar wanda yake wa nasiha ce fatansa,
sai dai zuciyarsa ta kunshe wani abu na daban sai ya karkata zuwa gare shi.
2. Khawarijawa sun kauracewa jama'ar musulunci da shugabansu, haka yan zanga-zanga da suka bar gidajensu da masallatan su, suka kaura
kan tituna da duwatsu, ko kungurumin daji.
3. Khawarijawa basa ganin ji da da'a ga shugabansu haka ƴan zanga-zanga.
4. Khawarijawa suna sukar majibicin al-amarin su haka yan zanga-zanga.
5. Khawarijawa sun raina magabata na kwarai, sai suka raya cewa sun fi Abdullah bnu Abbas Ilmi, haka yan zanga-zanga sun raina wadanda suke dore akan tafarkin magabata, suna danganta su da jahilci da rashin wayewa, sa'annan da kokarin mai da al-umma ba, don sun doru akan ingantaccen tafarki: na ilmi da karantarwa,
na zaman lafiya da ciki gaban addinin Allah da tsaftace shi daga kircin bidi'ah da son zuciya.
6. Khawarijawa mutane ne da suka karanta al qur'ani, amma basu fahimci sunnah ba, haka yan zanga-zanga, daga cikinsu akwai wadanda kwana sallah suke yi a wajen taron su, amma basu fahimci akan kuskure suke ba.
7. Khawarijawa sun wajabtawa mai haila azumi, ya zanga-zanga sun yi sassaucin jinkirta sallah a yayin zanga-zanga.
8. Khawarijawa suna kyautata magana, kamar; neman ayi adalci, suna boye mummunar manufa a karkashin maganganun su.
9. Khawarijawa suna iya neman taimakon kafirai domin yakar musulmai, haka yan zanga-zanga, suna neman taimakon arna domin a kauda shugabansu.
10. Khawarijawa Suna bata lokacinsu akan tanadi na barna, haka yan zanga-zanga.
11. Khawarijawa suna karyata masu hadisan manzon Allah da suke karantar da wajabcin da'a wa shugaba koda kafiri, haka yan zanga-zanga.
12. Khawarijawa basu damu da zubar da jini ba, haka yan zanga-zanga, basa martaba jinin jikin balle na yan uwansu, suna aiki da hanunsu domin jefa kansa da al-ummar su cikin wahala da rikici maras iyaka.
13. Khawarijawa masu kananan tunani ne, yara wadanda basu san ciwon kansu ba, balle na addininsu da al-ummar da suke rayuwa cikin ta, haka yan zanga-zanga.
Saboda haka, suka yi daidai wajen jefa al-umma cikin hargitsi da matsatsi.
Bayan abinda yake karkashin haka na sharri da makircin yahudawa da ke cikin motsin da ake a duk wata zanga-zanga da aka kulla.
Ba abinda yafi ciwo cikin wannan batu, sama da danganta wadanda suka mutu a fagen da shahada,
da itace mabarnatan malaman da suke kira zuwa ga fita zanga-zanga ke rudin jahilai, matasansu da tsofinsu.
Khateebul-baghdaadi yace:
'Ban taba ganin karyar data fi ta wadanda suke jingina kansu da alheri da zuhudu ba.'
Tabbas! Itace karyar da ma'abota rauni ke hawa kanta, hawan da ba wanda ya isa ya ture su sai dai mutuwa, itace take ta mankade duk wanda wani makaryacin malami ya dora akan karyar sa.
Allah ya yawaita su a wannan zamani: masu kira zuwa ga kofofin wuta a lahira da bakin bindiga a duniya.
Allah ya jarrabi al-umma da irinsu,
jarabawar da masu nasara cikinta sun karanta, sune kadan, wadanda in kayi tafiya dasu zaka tsira, in ka karkace ga barin tafarkinsu ka karkata, saboda tsananin rikon su da gaskiya har Allah yake sanya gaskiya akan harcensu.
Bugu da kari, idan al-amarin al-umma ya koma hanun masu wa'azi sun tabe, malamai sune magada annabawa,
masu wa'azi da kissoshi raunana,
masu zaburar da matasa akan shugabanninsu,
masu karya da sunan maslahar da'awa,
masu kokarin daidaita gaskiya da karya,
irin wadannan sanadiyyar su ne al-umma ta dare,
kimar tafarkin magabata ta sauka a idon mutane,
har suke danganta su da rashin kyakkyawan tsari, da iya makircin yaki, da kwarewa a zamantakewa.
Ya Allah kai masu abinda suka cancance shi.
IBRAHIM LAWAL
SORO
AL-AZHAR
UNIVERSITY, CAIRO, EGYPT
27/09/2013
No comments:
Post a Comment