Wednesday, 4 February 2015

Salafiyyah Ko Ikhwaniyyah?!




Ba wani malami mai fikra ta caji da ingizawa bai xanxani wani sashi na ikhwaniyanci ba! A ko'ina ya ke a faxin duniyar nan!

Hakan kuma ya samo asali ne daga khawarijancin da suke wakilta a wannan zamani.

Ba bu wata qungiyar addini -kamar suke faxa- mai tarin mabiya a kowace qasa take da qungiyar Ikhwan ba su kai musu caffa ba, har ga wasu  masu qaryar  salafiyyah, musamman a qasata!
Shi ya sa maganar Dan Uwa Sheikh Dr. Kabir Lawal take yawo kullum a zuciya ta idan an fara vatun da’awar salafiyyah; saboda waxanda suke vavatun Salafiyyar har aka sannu da sunanta, ba su da alaqa da da’awarta idan aka kyakkyawan tantancewa.

Ma’anar maganar Malam Kabir Lawal kuma ita ce:

“Da’awar Salafiyyah a Najeriya za a iya qiranta: Qutbiyyah Kharijiyyah . . .”
Saboda galibin waxanda suke furta wannan da’awa mai albarka ba su huce ga barin bamkama wasu gaggan ‘yan bidi’ah da son zuciya ba! Suna fushi in an tsoratar ga barinsu, suna korel ga malaman Salafiyyah ta gaske dare da rana.
Wata rana Xan Uwa Malam Habib Ibrahim yana mai liqa lokutan karatu na majlisin Sheikh Bashir Bn Nuh Assalafy na ga wani Ikhwanee ya bayyana yana mai tambayar a kan mai karantarwar da kuma garinsu, bayan ya sanya sunan sanin mafi kusan abokanansa, amma abin da na xauka tun a wancan lokacin shi ne:
jahiltar da kansa ya yi da gangan domin manufofi masu yawa, daga cikinsu akwai:

•    Wautarwa: hakan zai kai wasu tunanin ai tunda irin su malam wane ma ba su san shi ba, ka ga ashe ba malami ba ne da za a gabatar da kansa a kan maganganun wasu, kamar maganganun Dr. Ahmad Gumi da sauransu daga cikin ‘yan caji da hukunta tunani a kan nassi.

•    Tsokana: domin ya gwada mutuntarsa a tsakanin xaliban ilmi, hakan kuma bai sa wani ya fusata ba a sakamakon tambayar tasa ta izgilanci.
Allah ka sa mu wanye lafiya, ya qara fahimtar da mu tafarkin magabata na qwarai a kan komai a rayuwarmu.

Ibrahim Lawal Soro
Al-Azhar University, Cairo, Egypt
Faculty of Shari’ah and Common Law
24/01/15

No comments:

Post a Comment