1.1 Gabatarwa
Abu ne mai ban mamaki mutum ya yi karatu har digiri na uku a jami'ar muslunci ace ba zai iya alakanta sashin ƴan bidi'a da sashi ba, tare da bayyanar maganadinsu da iya ɓamɓare shi a tsananinsu wahalarsa tafi tsanani sama da tabbatar da rashinsu da wanzuwarsu.
Kodayake, dama akidar ya tara ba tare da tsari ba, ta yadda wata zata iya ɓace masa gabarin wata, don haka ban sha mamaki ba don ya sanya wadanda malamansa suka sanya su a matsayin na gaba-gaba a jerin yan bidi'a a wannan zamani, shi kuma yace almajiran Ibn Taimiyyah ne -in da sheikhul-islam yana da numfashi, da ya karyata shi-, saboda wannan ƙarya ce baka, da kowa yake ganinta, sai wanda Allah ya share ganin zuciyarsa, wanda ilmi ne rayuwarsa -wanda aka dauke shi, ba tare wasu maɓarnata ko son shahara ta farauci romonsa ba.
Sheikh Salih al-Fauzan -Allah ƙara masa lafiya- yace:
"MANHAJI YA FI AƘIDA FADI DA GAMEWA: DA SHI NE ZAKA MU'AMALANCI AKIDA, IBADA, MU'AMALA, SULUKI DA DABI'A . . . "
Abin mamaki shi ne abin da ire-irensa suka jahilta ko suka jahiltar da kansu, har suke fafarar dalibai gabarin malaman da suke karantar dashi, suke ƙoƙarin ɗora wadanda suka karkace gabarinsa.
Bugu da kara, ya kamata ace ire-irensa su yi wa masu saurarensu adalci, su yi musu rangwame, su bayyana musu gaskiya a yadda take ba tare da rufa-rufa ba.
1.2 Alaƙarsu Ta Bangaren Aƙida Da Tsari
Abu na farko da ya kamata kowa ya ƙara tabbatarwa shi ne:
matsotsarsu ɗaya ce: littattafan Sayyid Qutb; wanda shi ne uban gayya a wannan zamani na duk wani bakhawarije ko dan rakajin jihadi.
Sun hadu akan wadannan aƙidu da manufofi:
1- Kafirta Ma'abocin Zunubi: wacce aƙida ce sananniya ta khawarijawa, ta hanyarta ce suke ganin halaccin jininsa.
Shi ya sa, in suka samu dama suke kashe shi, kamar yadda suka yi a 70's 80's a Misra, kamar yadda suke yi yanzu, tsohuwar rigarsu ce da take rataye suka ƙara yabo ta.
In kace, 'ai yan Boko-Haram sun sun haramta siyasa da aikin gwamnati, sai nace, 'in da sun yi nisan zango a fagen ƙira da za su dawo kamar yadda ƴan uwansu Shi'ah suka yi, kuma ai ita ce hanyar kakarsu Ikhwan a farkon zango, har zuwan Rabi'ul Arabi, saboda suna ga tun da sune kanwa uwar gami, ba za su yi asara ba, gwamma a dama da su, sai malamansu da suke ganin shugabannin larabawa dagutai ne ƙarƙashin reshe na hudu da suka ƙirƙira wa tauhidi: "Tauhidul-Haakimiyyah, wanda malaman sunnah yi martani: Uthaimeen yace, 'yana daga cikin tauhidul-uluuhiyyah.
Tare da abin da suka kudurce na manufar dawowa da khadifancin muslunci kamar yadda suke rayawa, amma ta hanyar da bata dace ba, shi ya sa Sheikh Albani yace musu,
'TA HANYAR TASFIYAH DA TARBIYAH AKE SAMUN KARFI BA HARE-HARE DA LA'ANCE-LA'ANCE BA' wannan kuma hali ne na wadannan kungiyoyi shu'umai.
A karkashin haka ne suka shagalta da neman mulki ta kowace hanya.
Kamar yadda aka samu malamin Boko-Haram ya kafirta ma'aikacin kotu, haka aka samu malamin Ikhwan ya kafirta ma'abocin mu'amala da riba.
2- Duk wanda ya saurari karatuttuka na Shugaban boko-haram zai ji ba shi da wasu jama'a da yake kokarin kwatanta kansa da su, yake kokarin ɗora jama'arsa akan tsarinsu koma bayan al'Qaedah, Taliban da Ikhwan, bal, yafi fifita Ikhwan saboda ita ce ta haifi wadancan kamar yadda dalilai suka nuna.
Daga cikin littattafan da shugaban ya karantar da dalibansa akwai:
i- Ma'aalim Fit Tariq [Sayyid Qutb]
ii- Maaza Qaddamta Li-Din al-Lah? [Muhammad Hassan]
Idan ka duba zaka ga sune iyayen ruhi na Ikhwan;
- Na farko: shi ya jagorancesu a rigingimu da su ka faru a wancan lokaci a Misra.
- Na biyu: shi yake jagorantar wutar rike-rike da yake faruwa yanzu a Misra da abokansa, kamar yadda Muhammad Yusuf ya jagoranta, bayan ya ƙoshi da manhaji irin na su.
Ya sauke littattafai masu yawa, har na Hassan al-Banna, amma na takaita akan wadancan ne saboda shaharar su da mawallaffansu.
3- Tsoratar Da Amintattu: Wannan a fili yake, sun kware wajen yada ɓarna da tada hankalin al'umma ta hanyar ɗage-ɗagen bama-bamai da harbe-harbe.
4- Kashe Wadanda Ba su Ji Ba, Ba Su Gani Ba: A yayin harbe-harbensu da ɗage-ɗagen tsinannun bama-bamansu na tawaye da kashe musulmai ƴan uwansu.
Wani abokina yake faɗa min, kamar yadda shaidar gani da ido ya faɗa masa shima, 'lokacin da ƴan Boko-Haram suka kai hari garin Misau, wani daga cikinsu ya harbi wani bawan Allah yana zaune a gindin wata bishiya.
Nan aka ce masa ba ɗan sanda ba ne, sai yace, 'ai naga ya aske gemunsa kamar ɗan sanda, shi ya sa na harbe shi.'
Shin wane dalili ne yace, 'ka kashe duk wanda ya aske gemu.'
5- Kashe Sojoji Da Ƴan sanda: Shi ne abin da Ikhwan ta rayu akansa a shekarun baya, shi ne kuma abin da take rayuwa akansa a kwanakin nan, ba wanda ya san ranar tsayawarsa sai Allah.
Shi ne abin da Boko-haram take rayuwa akansa, har zuwa yau. Allah ya kawo mana karshensa.
Daga karshe, kai wanda baka san manhajin ahlus-Sunnah ba, ka yi ƙoƙarin sani, domin banbance su daga wasunsu, kar ka rude a rayuwa.

Ibrahim Lawal
Soro
Al-Azhar
University, Cairo, Egypt
01/02/2014
No comments:
Post a Comment