1.4 Alakar
Ingancin Rayuwa Da Tarbiyya Ta Gari
Tsayayye ba zai taba kama da zaunanne ba, kamar yadda motsi haka matacce yake a daskare, saboda kowa ne bangare sha'aninsa daban;
hankali da rashin sa wasu abubuwa ne masu fada da junansu; lamarin
tarbiyya da tabarbarewarta wane fage ne da yake bukatar masu ido cikinsa su tashi domin wayar da kan al-ummar da suke rayuwa cikinta, musamman
bangaren gyara alakar bawa da ubangijinsa, shine mafi tsadar bangaren,
mafi hatsarinsa idan aka jahilce shi,
ko aka san shi ba tare da anyi aiki dashi ba.
Mafiya yawan wadanda ke rubutu akan tarbiyya a yanzu sun fi karkata zuwa ga bangare gyara alakar bawa da yan uwansa, kamar: iyayensa, malamansa,
da duk wanda yake gaba dashi,
amma sun mance gyara alakarsa da wanda yake gaba da kowa
mahaliccin kowa Allah Madaukakin sarki da buwaya.
Rayuwa itace muke cikinta, ba shakka, tana bukatar ababen da zasu taimaka wajen tsawuwarta.
Abubuwan da suke taimaka mata kuwa sun rabu kashi biyu:
Na Farko: Abubuwa na zahiri, wadanda ake iya riskarsu da daya daga cikin gabban riska da fahimta ko hankalta.
Misali: Abinci, ruwa, da sauransu.
Suna taimakawa kwarai wajen inganta rayuwa da gina zahirinta.
Wannan shine abinda marassa addini da shagala suka fi damuwa dashi, sa'annan marassa sani ke la'akari dashi wajen banbance masu jin dadin rayuwa da akasinsu.
Ba shakka irin wannan hukunci ya taso ne bisa jahiltar halin da bangaren na biyu suke ciki, da rashin sanin tarin ni'imomin dake karkashin su.
Na Biyu: Na badini; shine numfashi, ma'ana: rayi wanda yake motsa gangar jiki, wacce abinci ke wa hidima.
A takaice, kamar yadda akwai abinda kewa gangar jiki hidima, haka akwai abinda ke wa rayin da ke motsa jikin hidima, amma duk cikin abubuwan banga ya musulunci ba: shaidawa ba abin bautawa bisa cancanta sai Allah, shaidawa annabi Muhammad Manzon Allah ne.
Gini akan wannan, ba wani dadi da kwanciyar hankali da wani zai samu a rayuwa in bai yi musulunci ba, musulmi yana cikin wadata a rayuwar sa matukar bai maida al-amarinsa ga wanin Allah ba.
Kamar yadda ruwa ke rayar da matacciyar kasa, haka imani da aiki yake raya kaikashasshen jikin da asalinsa dama kasa ce.
Bugu da kari, kamar yadda gangar jiki take bukatar ci da sha, haka rayi da tunin ya zama asalin rayuwa yake bukatar ci da sha,
na farko cinsa da shansa a fili yake, don haka yafi sauki mu'amala,
na biyu cinsa da shansa ta wata hanya ce da sai an lakanceta, sai an karanceta daga wajen masana, ma'abota amana da sadaukarwa.
Sai ya zam hanya ta farko ana saninta ce bisa lalura, ita ta biyu ta hanyar nazari ake tsinkayarta, a hanun masana, wandanda ke kokarin kiyaye bangarenta.
1.5 kammalawa
In dan uwa yayi dubi da idonsa mai ji da karba, zai fahimci wasu abubuwa kamar haka:
i- Tarbiyya zata iya tsayawa a matsayin rayuwa. Rayuwa zata iya maye gurbin tarbiyya amma ba a kowane lokaci ba.
Dalili akan jumlar farko shine: ma'anar tarbiyya itace; renon abu ta dago shi, ai haka dama rayuwa take; mataki-mataki ce.
Sai ya zamanto, duk wanda yake da tarbiyya ta gari: tarbiyyar sunnah, shike rayuwa da alheri, rayuwa mai amsa sunanta.
Dalili akan na biyu kuma shine: ba kowane lokaci ne wanda yake rayuwa ke da tarbiyya ba, shiya sa daga cikin wadanda suke rayuwa akwai matattu,
to amma in ana rayuwar za'a iya dacewar da tarbiyyar, saboda ita rayuwa mataki-mataki ce,
haka zalika tarbiyya, ma'abotan su suna iya daukaka, suna iya kaskanta; suna iya hawa suna iya sauka.
ii. Akwai wadanda suka fahimci tarbiyya da ma'anar makauniyar biyyayya.
Wannan fahimta kuwa ta yi muni; saboda a karkashin ta ake dushashe alherai masu din bin yawa.
Wadanda suka fahimci haka, sun san anyi wa addini illa a karkashin wannan mummunar fahimta.
Sau nawa mutane ke take na kasa dasu, su kwaci hakkinsu, su manta da hakkin mahaliccinsu?!
Sau nawa mutane ke maida gaskiya da sunan anyi nuna musu rashin tarbiyya?!
Sau nawa wasu ke jingina masu nusantar dasu da rashin tarbiyya; rashin kunya?!
iii. Yana daga cikin alamun mai tarbiyya:
- Sauke hakkin Allah, Manzonsa da sahabbansa dake kansa dana sauran bayin Allah.
- Mutunta ma'abota mutunci.
- Nisantar ma'abota sakaci da lalace a bangaren neman ilmi da aiki dashi.
- Riko da gaskiya da lazimtarta koda an samu sauyin zamani da makani.
- Son ci gaban al-ummar a addininsu; rayuwarsu ta duniya da lahira.
- Karantar da al-umma kana da yin hakuri dasu akan ƙura-kurensu da gyara su.
- Baya daga cikin dabi'arsu, kauracewa al-umma da wani suna ko aiki, wanda ya sabawa al-ummar muslunci.
Basu yarda da rarraba al-umma ba, saboda hatsarin aikin, da mummunar makomar mai yinsa.
iv. Kwanciyar hankalin mai tarbiyya ta gari, da bayyanar rauni na ma'abocin muninta.
v. Gamewar ma'anar tarbiyya izuwa ta gari da sabaninta.
A karkashin haka, abinda ya zama wajibi shine: idan an saki kalmar "tarbiyya" kamata yayi duk wani musulmi ya labartawa zuciyarsa; tarbiyyar musulunci ake nufi ba wata ba!
Alhamdullah!
24111434/29092013.

No comments:
Post a Comment