Ibnu Qudaamah
-Allah ya jikansa- yace:
وقد ذكر القاضى أن
التائب من البدعة يعتبر له مضي سنة : لحديث صبيغ بن عسل, رواه احمد فى الورع , قال: ومن علامة توبته
أن يجتنب من كان يواليه من اهل البدع, ويوالى من كان يعادى من اهل السنة."
" Ma'ana:
"Hakika alkali ['Iyyad] ya ambata [cewa]
lallai mai tuba daga bidi'ah ana la'akaranta masa shekara [domin aga gaskiyar
tubarsa]: saboda hadisin Sabiigh Dan 'Asl, Imam Ahmad ya rawaito shi a
aL-WARA', yace:
"Yana daga cikin alamar [kyan] tubarsa;
ya nisanci wanda yake jibinta daga cikin yan bidi'ah, ya jibinci wanda ya
kasance yake kiyayya da shi [a baya] daga cikin ahlus-sunnah."
Nace: Bisa abin da ya gabata zamu fahimci
abubuwa kamar haka:
1-
Taka-tsantsan magabata na kwarai ke yi da
bidi'ah da yayanta, saboda sanin hatsari da makirci da yaudararsu.
2-
Ana zura
ido wa dan bidi'ah na kimanin sheraka guda kafin samun nutsuwa dangane da
ingancin tubarsa. Mafiya yawan wadanda suka bata addinin Allah yawacinsu
tubabbu ne, ina nufin wadanda suka yi wani addini kafin musulunci, sau da dama
suna haurowa musulunci da akidar addininsu. Abdullah Bn Saba'I babban misali
ne, da wasu turawa a wannan zamani, da kuma jiga-jigan yan bidi'ah da tsakinsu.
3-
Kaurace
wa abokan barna yana saurin tafiyar da tasirinta ga barin tubabbenta.
4-
Tarayya da su bayan tuba yana nuna yarda da
abin da suke ka yi na barna, da kuma yiwuwar komawa cikinta.
5-
Dan bidi'ah makiyin ahlus-sunnsh ne, da akasin
haka.
6-
Da haka
mutuncin sunnah zai dawo, ba da ruwantar da manhajin magabata na kwarai ba; ta
yadda wasu ke inuwantar da su bisa wa su muggan ka'idoji wadanda wasu shedanu
yan ruwantarwa suka kulla.
Ibrahim Lawal Soro
Al-Azhar University, Cairo, Egypt [5/May/2014]
No comments:
Post a Comment