Wednesday, 4 February 2015

Wata Nasiha Da Tunatarwa



Salafiyyah ba qungiyanci ba ce; bauta wa Allah (S. W. T) bisa karantar littafinsa, sunnar Manzonsa (S. A. W), da magabata na qwarai da wad'anda su ke binsu da kyautatawa shi ne salafiyyanci.

qoqorin voyayyun an k'ungiya na k'ungiyantar da ita, in sha Allah, zai ci tura, saboda Allah ya azurtata da dakarun da ba sa jin tsoron zargin mai zargi, su na da jarumtar k'arbar bak'onci, kuma sun sani sarai; bak'oncinsu ba zai kai d'aya bisa biyun na wad'anda su ka gabace su ba.

Yana daga cikin abin da ta keb'anta daga watanta da shi: hak'urtarwa ga mabiyanta dangane da nasara mai gangarowa koda a bayan ransu, sabanin wasu jama'un da ke son ganin tasirin abin da su ka yi k'ira zuwa gare shi nan take.

Bisa ga abin da ya ke sama: in da al-All
āmah al-albānī, al-allāmah Bn Bāz, al-allāmah Uthaimīn, da sauran wad'anda su ka d'auki da'awar salafiyyah a kafad'unsu, kamar al-allāmah Āli al-Jāmē, za su lek'o wannan duniya da farin cikinsu ya k'aru a kan wanda su ka shud'e akansa sakamakon abin alherin da su ka dasa wa al'ummar Annabi (S. A. W).

Tare da yaguni irin da na kuluyoyi ga wannan da'awa da wasu ke yi kullum ba shi zai sa ta risina wa firgitarwarsu ba.

Ka sani d'an uwa: ba fa'ida cire hannu daga wani aikin alheri wanda farkonsa ya ke alak'a da k'arshensa ko waninsa, saboda haka in ka kasance a kan tafarkin gaskiya ka shud'e akansa.

Ina k'ira gareku:

Y
ā salafāwa na gaske
Kar ku y
ō yarda a cafke
Ak'idarku ko a damk'e
Hanjinku da 'yan silalla!

Kafin na kammala zan so 'yan uwa su yi domin zuwa ga kalmar al-All
āmah al-Albānī da ke tafe, ina kuma sa ran 'yan uwa za su fahimce ta, fshimtarta zai taimaka musu akan halin da su ke ciki yanzu na tab'arb'arewar al'amura da nufatarsu zuwa ga lalacewar da zai an sha matsananciyar wuyar da ba za a iya kwatantawa ba kafin a shawo kanta.

al-All
āmah al-Albānī -yana mai bayyana hanyar tsira da samun nasarar al'ummar musulmai da martani ga matasan da su ka d'auki ak'ida da manhajin khawarijawa- ya ce:

"
ﺇﻥ ﺍﻟﺨﻼﺹ من ﺃﻳﺪﻱ ﻫﺆﻻﺀ
ﺍﻟﺸﺒﺎﺏ ﻳﺘﻤﺜﻞ ﻓﻲ ﺃﻣﺮﻳﻦ ﻻ ﺛﺎﻟﺚ ﻟﻬﻤﺎ ؛
ﺍﻟﺘﺼﻔﻴﺔ ﻭﺍﻟﺘﺮﺑﻴﺔ .
ﺍﻟﺘﺼﻔﻴﺔ: ﻭﺃﻋﻨﻲ ﺑﺎﻟﺘﺼﻔﻴﺔ: ﺗﻘﺪﻳﻢ
ﺍﻹﺳﻼﻡ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺸﺒﺎﺏ ﺍﻟﻤﺴﻠﻢ ﻣﺼﻔﻰًّ ﻣﻦ
ﻛﻞ ﻣﺎ ﺩﺧﻞ ﻓﻴﻪ ﻋﻠﻰ ﻣِّﺮ ﻫﺬﻩ ﺍﻟﻘﺮﻭﻥ
ﻭﺍﻟﺴﻨﻴﻦ ﺍﻟﻄﻮﺍﻝ؛ ﻣﻦ ﺍﻟﻌﻘﺎﺋﺪ ﻭﻣﻦ
ﺍﻟﺨﺮﺍﻓﺎﺕ ﻭﻣﻦ ﺍﻟﺒﺪﻉ ﻭﺍﻟﻀﻼﻻﺕ، ﻭﻣﻦ
ﺫﻟﻚ ﻣﺎ ﺩﺧﻞ ﻓﻴﻪ ﻣﻦ ﺃﺣﺎﺩﻳﺚ ﻏﻴﺮ
ﺻﺤﻴﺤﺔ ﻗﺪ ﺗﻜﻮﻥ ﻣﻮﺿﻮﻋﺔ، ﻓﻼ ﺑﺪ ﻣﻦ
ﺗﺤﻘﻴﻖ ﻫﺬﻩ ﺍﻟﺘﺼﻔﻴﺔ؛ ﻷﻧﻪ ﺑﻐﻴﺮﻫﺎ ﻻ
ﻣﺠﺎﻝ ﺃﺑﺪﺍً ﻟﺘﺤﻘﻴﻖ ﺃﻣﻨﻴﺔ ﻫﺆﻻﺀ المسلمين. . "


"Lallai tsira daga hanun wad'ancan samari yana misalta da abubuwa guda biyun da ba na uku gare su:

1-Tasfiya da
2-Tarbiyya.

1-Tasfiya: abin da na ke nufi da Tasfiya: gabatar da musulunci ga samari musulmai (wanda ya zama) tatacce daga dukkan abin da ya shiga cikinsa a tsawon K'arnuka da dogin shekaru; na (gurbatattun) ak'idu, (kama) daga kan tatsuniyoyi, bidi'o'i da b'ata.

Yana daga cikin haka: abin da aka shigar a cikinsa na hadisan da ba ingantattuba, zai iya yiwuwa ma su k'agaggu ne, saboda haka ba bu makawa (sai) an tabbatar da wannan tsarkakewa, domin da waninta ba bu damar tabbatuwar burace-buracen wadancan musulman har abada (yana nufin khawariyan da su ke yak'i a Afgh
ānistan)."

Sa'annan Ya ci gaba da cewa:


"
ﻓﺎﻟﺘﺼﻔﻴﺔ ﻫﺬﻩ ﺇﻧﻤﺎ ﻳﺮﺍﺩ ﺑﻬﺎ ﺗﻘﺪﻳﻢ
ﺍﻟﻌﻼﺝ ﺍﻟﺬﻱ ﻫﻮ ﺍﻹﺳﻼﻡ، ﺍﻟﺬﻱ ﻋﺎﻟﺞ ﻣﺎ
ﻳﺸﺒﻪ ﻫﺬﻩ ﺍﻟﻤﺸﻜﻠﺔ، ﺣﻴﻨﻤﺎ ﻛﺎﻥ ﺍﻟﻌﺮﺏ
ﺃﺫﻻﺀ.
"Wannan Tasfiyar iyaka abin da ake nufi da ita gabatar da maganin da shi ne (karantarwar)musulunci, wanda ya magance irin wannan mushkila a yayin da larabawa suka kasance k'ask'antattu"

Ya kara akan haka:

"
ﺃﻣﺎ ﺃﻥ
ﻧﺒﺪﺃ ﺑﺎﻷﻣﻮﺭ ﺍﻟﺴﻴﺎﺳﻴﺔ، ﻭﺍﻟﺬﻳﻦ
ﻳﺸﺘﻐﻠﻮﻥ ﺑﺎﻟﺴﻴﺎﺳﺔ ﻗﺪ ﺗﻜﻮﻥ ﻋﻘﺎﺋﺪﻫﻢ
ﺧﺮﺍﺑﺎً ﻳﺒﺎﺑﺎً، ﻭﻗﺪ ﻳﻜﻮﻥ ﺳﻠﻮﻛﻬﻢ ﻣﻦ
ﺍﻟﻨﺎﺣﻴﺔ ﺍﻹﺳﻼﻣﻴﺔ ﺑﻌﻴﺪﺍً ﻋﻦ ﺍﻟﺸﺮﻳﻌﺔ ،
ﻭﺍﻟﺬﻳﻦ ﻳﺸﺘﻐﻠﻮﻥ ﺑﺘﻜﺘﻴﻞ ﺍﻟﻨﺎﺱ
ﻭﺗﺠﻤﻴﻌﻬﻢ ﻋﻠﻰ ﻛﻠﻤﺔ ( ﺇﺳﻼﻡ ) ﻋﺎﻣﺔ
ﻟﻴﺲ ﻟﻬﻢ ﻣﻔﺎﻫﻴﻢ ﻭﺍﺿﺤﺔ ﻓﻲ ﺃﺫﻫﺎﻥ
ﻫﺆﻻﺀ ﺍﻟﻤﺘﻜﺘِّﻠﻴﻦ ﺣﻮﻝ ﺃﻭﻟﺌﻚ ﺍﻟﺪﻋﺎﺓ،
ﻭﻣﻦ ﺛﻢ ﻟﻴﺲ ﻟﻬﺬﺍ ﺍﻹﺳﻼﻡ ﺃﻱ ﺃﺛﺮ ﻓﻲ
ﻣﻨﻄﻠﻘﻬﻢ ﻓﻲ ﺣﻴﺎﺗﻬﻢ، ﻭﻟﻬﺬﺍ ﺗﺠﺪ ﻛﺜﻴﺮﺍً
ﻣﻦ ﻫﺆﻻﺀ ﻭﻫﺆﻻﺀ ﻻ ﻳﺤﻘﻘﻮﻥ ﺍﻹﺳﻼﻡ
ﻓﻲ ﺫﻭﺍﺕ ﺃﻧﻔﺴﻬﻢ، ﻓﻴﻤﺎ ﻳﻤﻜﻨُﻬﻢ ﺃﻥ
ﻳﻄﺒِّﻘﻮﻩ ﺑﻜﻞ ﺳﻬﻮﻟﻪ . ﻭﻓﻲ ﺍﻟﻮﻗﺖ ﻧﻔﺴﻪ
ﻳﺮﻓﻊ ﻫﺆﻻﺀ ﺃﺻﻮﺍﺗﻬﻢ ﺑﺄﻧﻪ ﻻ ﺣﻜﻢ ﺇﻻ
ﻟﻠﻪ، ﻭﻻ ﺑﺪ ﺃﻥ ﻳﻜﻮﻥ ﺍﻟﺤﻜﻢ ﺑﻤﺎ ﺃﻧﺰﻝ
ﺍﻟﻠﻪ؛ ﻭﻫﺬﻩ ﻛﻠﻤﺔ ﺣﻖٍّ، ﻭﻟﻜﻦ ﻓﺎﻗﺪ
ﺍﻟﺸﻲﺀ ﻻ ﻳﻌﻄﻴﻪ . . "

"Amma ace mu fara da siyasa, wad'anda suke shagalta da siyasa zai iya yiwuwa ak'idarsu ta kasance rushewa da tabarbarewa, kuma tsarin gudanar da al'amuransu ta b'angaren musulunci ya yi nisa gabarin shari'ah, har ilau wad'ancan da suke shagalta da farautar mutane da haka a karkashin kalmar (musulunci) a jumlace, ba su da wata fahimta (manufa) fayyatacciya dangane da kwakwalen wad'ancan da aka farauta a gaban wad'ancan masu kira, kuma musuluncin ba shi da wani tasiri akan gangarawarsu (hidimominsu) a cikin rayuwa, saboda haka ne za ka iske wad'ancan da wad'ancan ba sa aiwatar da (karantarwar) musulunci a karan-kansu dangane da abin da za su iya samun damar aitawar da shi da dukkan sauk'i.

A cikin (wannan) lokacin shi kansa, za ka ji wad'ancan suna d'aga sautukansu da cewa: 'lallai ba hukunci sai na Allah, ba bu makawa sai anyi hukunci da abin da Allah ya saukar . . ' wannan maganar gaskiya ce, sai dai maras abu ba ya bada shi!"

Daga bisani ya kawo na biyu, yace:

"
ﺍﻟﺘﺮﺑﻴﺔ: ﻭﺍﻟﺸﻄﺮ ﺍﻟﺜﺎﻧﻲ ﻣﻦ ﻫﺬﻩ ﺍﻟﻜﻠﻤﺔ
ﻳﻌﻨﻲ ﺃﻧﻪ ﻻ ﺑﺪ ﻣﻦ ﺗﺮﺑﻴﺔ ﺍﻟﻤﺴﻠﻤﻴﻦ
ﺍﻟﻴﻮﻡ، ﻋﻠﻰ ﺃﺳﺎﺱ ﺃﻻ ﻳﻔﺘﻨﻮﺍ ﻛﻤﺎ ﻓُﺘِﻦ
ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻣﻦ ﻗﺒﻠﻬﻢ ﺑﺎﻟﺪﻧﻴﺎ . ﻭﻳﻘﻮﻝ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ
ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﻭﺍﻟﺴﻼﻡ: ( ﻣﺎ ﺍﻟﻔﻘﺮ ﺃﺧﺸﻰ
ﻋﻠﻴﻜﻢ ﻭﻟﻜﻦ ﺃﺧﺸﻰ ﻋﻠﻴﻜﻢ ﺃﻥ ﺗُﻔﺘﺢ
ﻋﻠﻴﻜﻢ ﺯﻫﺮﺓ ﺍﻟﺤﻴﺎﺓ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ، ﻓﺘﻬﻠﻜﻜﻢ ﻛﻤﺎ
ﺃﻫﻠﻜﺖ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻣﻦ ﻗﺒﻠﻜﻢ ). ﻭﻟﻬﺬﺍ ﻧﺮﻯ ﺃﻧﻪ
ﻗَّﻞ ﻣَﻦْ ﻳﻨﺘﺒﻪ ﻟﻬﺬﺍ ﺍﻟﻤﺮﺽ ﻓﻴﺮﺑﻲ
ﺍﻟﺸﺒﺎﺏ، ﻻ ﺳﻴﻤﺎ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻓﺘﺢ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻬﻢ
ﻛﻨﻮﺯ ﺍﻷﺭﺽ، ﻭﺃﻏﺮﻗﻬﻢ ﻓﻲ ﺧﻴﺮﺍﺗﻪ . . . "

2-"Tarbiyya: sharadi na biyu daga wannan magana yana nufin ba makawa; tarbiyantar da musulman yau, don kar a fitine su da duniya kamar yadda aka fitini wadanda suka zo gabaninsu.

Manzon Allah (S.A.W) yana cewa:

"Ba talauci nake tsorata muku ba, sai dai ina tsorota muku ace k'awar rayuwar duniya ta bud'e muku, sai ta halakar daku kamar yadda ta halakar da wadanda su ka zo kafin ku"

saboda haka muke ganin sun k'aranta wad'anda su ke fad'aka da irin wannan ciwo balle su tarbiyantar da matasa.
Musamman wad'anda Allah ya bude musu taskokin k'asa, ya nutsa su a cikin alheransa."

A karshe: burin kowa daga cikin d'aid'aiku shi ne tsira, ina ga al'umma gaba d'ayanta?!
Saboda haka ya zama wajibi ga wani ko wata al'umma ta kama hanyar tsira da ta sani ita ce aka zayyana a littafin Allah, sunnar manzonsa, fahimtar magabata na kwarai, da wata hanya da ba ta sab'a wa wad'ancan ba!
Amma rik'ewar wasu ga al'amarin mutane kana da wargaza shi cin amana ce, saboda musulunci ya zo da mafi buk'atar mutane: sanin Allah wanda da shi ne kai ya ke had'uwa, a sakamakon haka ne ya zama wajibin duk wani mai k'ira farawa da shi kafin gangarawa waninsa.

A tak'aice, ina k'ira ga 'yan uwa da su zama masu bibitar tafarkin magabata na kwarai da kauce wa waninsa, domin nasara tana zuwa daga haka, kuma na farko dangane da al'amarin tushen addini da tafarkinsa bai bar wa na karshe komai ba!

Ya Allah ka k'arfafa wannan al'umma rarrauna da irin abin da ka k'arfafa na farkonta.

Ibrahim Lawal Soro
al-Azhar University, Cairo, Egypt
Faculty of Shari'ah and Common Law
23/12/2014

No comments:

Post a Comment