Wednesday, 4 February 2015

Fitinar K'ungiya Da K'ungiyanci





Musulunci kamammen gini ya ke kafin diga-digan rushewa su bayyana; sun zo da abin da ya ke juya halitta daga asalin tsarinta zuwa ga wani shiri na tsirarunta. A kullum idan ka lura da motsin wata k'ank'antacciyar al'umma za ka iske sab'awar mutanenta yana cikin dalilan rauninta, kuma k'arfinta ko akasinsa yana da alak'a da raguwa ko k'aruwa a kan abin da ambatonsa ya gabata.

Bugu-da-k'ari, a lokacin da turawan mulkin mallaka suka ratso cikin al'ummar musulunci abu na farko da suka fara kafawa kafuwar tuken rago shi ne: tabbatuwar rabuwarsu zuwa k'ananan k'asashe da za su yi birgimar mad'ud'un shekaru da ba su kamo idon sawunsu ba, duk k'ok'arin wurgar da addininsu da al'adunsu da suka yi, wannan batu kuma a fili ya ke, wad'anda suka gabata sun shanshane shi, mu kuma a yau muna d'and'anarsa.

Bisa ga abin da ya ke sama, a nan zan kawo d'aya daga cikin hanyoyi da kucikoki da irin wad'ancan allurorin b'ula afolon had'in kan al'umma suke amfani da shi domin dawo da al'umma baya, sanya ta a cikin k'angi, da ganin banza wanda ya ke tasowa daga mabambantan b'angarorinsu:

-Kafirai wadanda ba su rigaya sun shiga musulunci ba,
-Musulman da suka jahilci musulunci,
-Musulman da suka jahiltar da kansu, da
-'Yan bidi'ah da son zuciya gaba d'ayansu sun yi taraiya wajen farka tsaftataciyar karantarwar addinin da ya d'auke su.

Abin mamaki; za ka iske kowanne daga cikin wadanda ambatonsa ya gabata yana da wani sashi na k'iyayya ga wad'anda suka tashi ka'in-da-na'in domin dawo da ruhinsa a bisa kalarsa da magabata na k'warai suka mik'o shi daga wajen wad'anda suka gabace su da kyautata har zuwa ga Manzon Allah (S.A.W). Daga cikin abin da zai baka mamaki shi ne: zagin irin wad'annan malamai da wad'ancan suke yi da munanan zagi, tare da tarin k'ok'orisu, ladabinsu, adalcinsu, da kyakkyawar manufarsu ga musulunci da musulamai.

Daga cikin mazagan nasu daga shagwab'abben da zai bayyana da k'aryar wayewa, kana da jifansu da k'auyanci, ko kuma wanda zai hauro a kan dokin son zuciya mai sukuwa a kan wani sashin ingantattun dalilai da kora su zuwa ga makwankwad'ar  b'ataccen tawili. 

al-Allaamah Muqbil Bn Hadee (R.A) ya ce:

إذا رأيت الرجل يسب علماء السنة فاعلم أنه مفتون، وأن الحزبية متغلغلة من قلبه وإن تظاهر بأنه سني"
".
 "Idan kaga mutum yana zagin malaman sunnah, [ya kamata] ka san wanda aka fitine shi ne [a kan addininsa], kuma lallai kungiyanci yana shawagi a cikin zuciyarsa, koda [kuwa] ya ta bayyana shi ma'abocin sunnah ce." (1)

Na ce:

Allah ya jikan al-Allaamah al-Muhaddith al-Jazeerah, irin wadannan fitinannu su a wannan zamani da malaman sunnah ta gaske suka karanta, su suka yi banga-banga a dandalin amsa sunan sunnah da kira zuwa gare ta har ake dangana shagwabarsu da ita dare da rana.

K'ari a kan haka: munmunan wakilcin da suke yi wa sunnah; zagin malaman sunnah tare da ik'irarin sunnah ya fi k'iran malaman bidi'ah zuwa ga bidi'arsu, domin ba za a rasa wanda Allah (S.W.T) zai rayar da shi, kana ya karfafe shi da makamai, kamar: ilmi, hikima, hak'uri, da juriya domin dirkake bidi'arsu ba!
Mun ga haka a rayuwar magabata na k'warai da wad'anda suka biyo su da kyautata, a wannan b'angaren kenan, wani b'angare kuma:

Ba kowa ya ke iya karb'ar rotse a kan wad'anda suka bayyana da sunan sunnah ba sai 'yan kad'an, sai lamarin ya zamanto kafin Allah ya ganar da mafi yawan mutane hatsarinsu sun yi wa sunnah b'arnar da gyara ta zai d'auki shekarun da ba a san iyakacinsu ba. Misali: Barnar da kungiyar Ikhwan da malamanta suka yi wa sunnah yaushe aka san ranar da za a gyara ta; tare da k'ok'arin malaman sunnah dare da rana a fagen wayar da mutane hatsarinsu?!

Bisa ga abin da ya ke sama, zamu fahimci wasu abubuwa kamar haka:

1- Zagin malaman sunnah fitina ce mai girma a rayuwar mutane; k'ok'orin dushashe hasken addini ne wanda wad'annan malamai suke d'auke da shi, saboda haka; zagwanyar da su zagwanyar da abin da suke d'auke da shi ne, shi ya sa don wanda ya dumfari wani malamin sunnah da cin mutunci sunnah ya dumfara da shi, kamar yadda lamarin ya ke ga ma'abocin zagin sahabban mazon Allah (S.A.W) da matansa (R.A).

2- Ba bu wanda d'osani kungiyanci da ba tantirin kansa ba ne: shi ya sa malamai suka tsoratar a kan mu'amalantar 'yan k'ungiya domin kar su tsarma wani sashi na shubuharsu a zuciyarka; tsarkake malamansu da jefa ra'ayin k'yamar maganganun wasunsu. A kan wannan batu ka tambayi duk wani gasasshen d'an kungiya zai ba ka lamari.

3- Mutane suna son bayyana da sunnah, saboda tabbataccen d'iso da ya ke zuciyarsu a kan ingancin magangararta koda sun jahilce ta ko sun jahiltar da kansau. Wannan bayyana ta su ba za ta basu lasisin zama ma'abotanta ba matuk'ar maganganunsu, k'udirinsu, da ayyukansu ba su dace da irin nata ba! Haka ma soyayyarsu, k'iyayyarsu, da bada kariyarsu ta zama a kanta suke yi, kuma dominta, amma idan ka ga wani shu'umi da sunan malumta yana tsoratarwa ga barin malaman sunnah; masu hidima a gare ta da bayyana duk wani sharri da aka nuface ta shi, ka san wannan b'oyayyen d'an k'ungiya ce, hukuncinsa hukuncinsu ne, koda makwancinsu ya bambanta: yana dawowa cikin ma'abota sunnah bararraje saboda makirci da barnatarwa.

4- 'Yan uwa ma'abota sunnah ya zama wajibi a kanmu; bada kariya ga sunnah da duk abin da muka mallaka na makamin ilmi, basira, hikima, da juriya.

5- K'ungiyanci shi ne sanadiyyar rabuwar kan musulmai a lokacin da ya shud'e, wanda muke ciki, da mai zuwa, in ba Allah ya tseratar da bawansa ba, in ya fad'a sai ta yi tabo a cikinsa koda ba kowa ya ke iya gane shi ba sai wad'anda Allah (S.W.T) ya horewa lak'antar motsinsu; wad'annan kuma su ne masu bayyana wa al'umma hatsarinsu, kuma ya zama wajibi ga wannan al'umma da saurara maganganunsu matuk'ar tudun mun tsira a salin'alin take nufi har a k'ark'ashin k'ahon zuciyarta.

 A k’arshe, wannan wata fa'ida ce da za ta amfanar a wannan sashi, kuma za a iya kintata ta a wasu sashuka na daban, matuk’ar an samu mahad’i: Ba duk wanda ya k'ira kansa ma'abocin sunnah ba ce ake saurara wa maganarsa matuk'ar k'udurinsa, manhajinsa, maganganunsa, da ayyukansa ba su dace da na sunnah ba! A sakamakon haka ne gaggan 'yan bidi'ah suka yi k'wayayyayi a cikin rumbun sunnah har suka fafe abubuwan da muke gani a yanzu. Mu fad'aka, mu fad'akar domin mu gudu tare, mu tsira tare.
Tushe Bincike:
(1) Kaset d’in tambayoyi a kan jihadi daga Birtaniya (1-10/170).

Ibrahim Lawal Soro
al-Azhar University, Cairo, Egypt
Faculty of Shari'ah and Common Law
29/January/2015.


No comments:

Post a Comment