Raka'o'in Alfijir suna ne na wata sallar nafila wacce Manzon Allah (S. A. W) ya lazimce ta bayan fitowar alfijir (tare da kiran sallah) kafin sallar asubahi, kuma ya tabbatar da ingancin yinta bayan sallar asubahi.
Bugu da kari: Dalilin ambatonta da 'Raka'o'in Alfijir' bai wuce cudanyarta da shi ba, sa'annan da kasancewarta takaitacciya ta fuskar karancin raka'o'i da karancin lokacin da ake dauka a ya yi gabatar da ita.
A kansa: A'ishah (R. A) da siffanta mana karancin lokacin da Manzon Allah (S. A. W) yake dauka da nuna zatonta a kan cewa: shin yana karanta fatiha kuwa?! Saidai hakika ta san sallah kowace iri ce bata yiwuwa saida karatun fatiha hatta sallar jana'izah saboda gamewar fadin Manzon Allah (S. A. W), kamar yadda ya zo a cikin 'Saheeh' (723), ya ce:
"لا صلاة لمن لم يقرأ بفاتحة الكتاب"
"Babu sallah ga wanda bai karanta mabudin littafi ba"
-Mabudin littafi ita ce 'Soorah al-Faatihah', littafin kuma shi ne 'al-Qur'aan al-Kareem'.
Kuma tana da falalar da ta kai matakin fin duniya da abin da yake cikinta.
Manzon Allah (S. A. W), kamar yadda ya zo a cikin 'Saheeh Muslim' (362), ya ce:
"ركعتا الفجر خير من الدنيا وما فيها"
"Raka'o'i biyu na alfijir sun fi duniya da abin da yake cikinta albarka"
Wannan falala makamanciyarta kadan ce a cikin ayyukan lada: Allah (S. W. T) ya halicci duniya, sa'annan ya halicce ka a cikinta, kuma ya yi maka nuni ga wani aikin alheri ta hanyar Manzonsa (S. A. W) wanda ya fi ta albarka; hakika wannan ba karamar falala ba ce wacce ta cancanci godiya mai yawa.
Domin bada wannan rubutu hakkin takensa, lallai A'ishah (R. A), kamar yadda ya zo a cikin 'Saheeh' (1110), ta ce:
"لم يكن النبي -صلى الله عليه وسلم - على شىء من النوافل أشد منه تعاهدا على ركعتي الفجر"
"Manzon Allah (S. A. W) bai taba kasancewa mai tsananin lazimtar wani abu na nafila ba sama da raka'o'i biyu na alfijir"
Wannan hasidi ya tara fa'idoji masu yawa, daga cikinsu:
1. Lazimtar Manzon Allah (S. W. T) ga wata Ibada yana fa'idantar da darajarta a matakin farko, sa'annan da wajabcinta idan ya wajabta ta, ko karfinta koda bai wajabta ta ba.
Misalin wancan ita ce Sallar Wutiri da wasu ibadu wadanda Manzon Allah (S. A. W) ya lazimce, har wasu mazhabobi suke ganin wajabcinsu, saidai abin sani: Akwai wanda aka farlanta masa, mu kuma aka sunnanta mana, ma'ana a hakkinsa farilla ce, mu kuma a hakkinmu sunnah ce, ana butakar zuwanmu da ita, koda bai kasance ba, babu wani laifi, kamar: (Sallar) Tsaiwar dare ko Tahajjud.
2. Ibada ta rabu gida biyu (2) ta wannan fuska, kamar haka:
i. Farilla ko wajibi: Ita ce zancen Mai Shar'antawa wanda yake rataye da neman wani abu da sigar 'yi' ko 'bari' bisa tilasci.
A karkashin wannan akwai umarni da hani, domin idan aka umarce ka da wani abu ya zama wajibi a kanka aikata shi, haka ma hani ya zama wajibi a kanka kamewa gabarinsa.
Ana bautawa Allah (S. A. W) da kowane a cikinsu, misali: Ya zama wajibi ka yi bauta da tsantsar tauhidi ga Allah (S. W. T), kamar yadda ya zama wajibi ka nisanci shirka kowace iri da kofofinta.
ii. Nafila: Ita ce abin da Mai Shar'antawa ya yi umarni da shi ko hani da shi ba bisa tilasci ba, ta yadda idan ya aikata shi zai samu samu lada, idan ya ki aikatawa kuma ba shi da zunubi, da akasin haka.
Hakika ma'anar nafila ita ce kusan ma'anar sunnah a wajen masana fikihu, tare da cewa akwai dan bamabanci kamar haka:
-Ita Nafila kamar kari ce a kan farilla, ma'ana: Bayan ka aikata abin da aka umarce ka da aikata shi bisa wajabci, sa'annan kuma sai ka zo da kari a kansa da abin da aka umarce da shi bisa zabin aikatawa ko barinsa.
-Da ita ake cike gibin da mutum ya yi a cikin farillunsa, sa'annan duk wanda ya cudayanta da ita dole ya zo da farillan da suke cikinta.
Misali: Wanda ya fara sallar Nafila dole ya zo da farillar karanta fatiha, ba zai ce tunda sallar nafila ce ba dole sai na karanta ta ba.
-Nafila hada wasu ibadu wadanda shari'ah ta yi umarni da su ba bisa tilas ba, su kuma suna kunshe da farillu da sunnoni a cikinsu wadanda suka zama wajibi ga wanda ya cudaya da ita zuwa da su kamar yadda yadda ya gabata, ragi ko kari a kansu bidi'ah ce, kuma suna bata su kamar yadda suke bata farilla.
-A yayin da sunnah kuma ta zama cikamakin ibadu na farilla da nafila.
-Rashin zuwa da ita a cikin mafiya yawan ibadu ba ya bata ta, saidai ya rage lada ko a bukaci mikar da ita da wani aiki da aka tanada domin haka.
-Wannan sunnah kenan a wajen masana fikihu, amma a wajen masana hadisi ta game koyi da Manzon Allah (S. A. W) a kan komai na fadinsa, da aikinsa, da tabbatarwarsa, da siffa ta dabi'arsa da ta halinsa.
A kansa: Duk abin da ya tabbata Manzon Allah (S. A. W) ya fade shi, ko ya aikata shi, ko ya tabbatar da shi, ko ya siffanta da shi a dabi'unsa, ko ya kasance siffarsa ta halitta, lallai ana kokarin koyi da shi matukar wani dalili bai tsaya a matsayin mai kebance shi, daidai ne ya yi umarni da haka ko bai yi ba, saboda gamewar fadin Allah (S. W. T) a cikin 'Soorah al-Ahzaab' (21), ya ce:
"لقد كان لكم فى رسول الله أسوة حسنة لمن كان يرجو الله واليوم الآخر وذكر الله كثيرا"
"Hakika kyakkyawan abin koyi ya kasance a gare ku a cikin (rayuwar) Manzon Allah ga wanda yake fatan Allah (da ayyukansa) da ranar karshe, kuma ya ambaci Allah da yawa"
Hakika komai a cikin rayuwar Fiyayyen Halitta (S. A. W) abin koyi ne, saidai akwai abubuwan da Allah (S. W. T) ya kebance shi da shi, ko yi da shi a kansu zai iya zama Haram, kamar: Auren sama da mata hudu, ko tsanantawa kai, kamar: Tsaiwar Dare a kullum duk tsanani da matsatsi da mutum ya samu kansa.
3. Raka'o'in Alfijir guda biyu suna da matsayi na musamman a wajen Manzon Allah (S. A. W), abin da yake tabbatar da haka shi ne lazimtarsa (S. A. W) gare su, saboda abin da suke kunshe da shi na lada mai tsoka, sa'annan da kwadaitarwarsa ga al'ummarsa lazimtarta a kowane lokaci, bal kwadaitarwar tasa gare ta ya kai ga lamince mata gabatar da ita a sabanin lokacinta idan ba a riske shi a sakamakon wani uzuri da Shari'ah ta amince da shi.
Allah ya yi mana baiwar lazimtar Sunnonin Manzon Allah (S. A. W) a cikin rayuwarmu.
©Ibrahim Lawal Soro
11. 02. 2017 C. E
No comments:
Post a Comment