Tuesday, 5 March 2024

Wata Fa'ida Ta Manhajin Salafiyyah

 


Tsoron maganar wasu mutane ba ya hana ma'abota gaskiya aiki da gaskiya koda sune marinjaya ta fuskar yawa da karfi, kamar yadda aikin makaryata da wani sashi na gaskiya ba ya hana magaskata aiki da ita, koda sun yi tarayya da su a wajen aiwatar da ita, amma hakan ba ya nuna tarayyarsu a kan tafarkinsu.

Dan uwa! Da wannan ka'ida Salafawa suke wanzuwa, kuma ta hanyarta suke dacewa da nasarori a fannin neman ilmi da aiki da shi.

Tabbas kangarewa wannan ka'ida mafari ne na 'Ruwantar da tafarkin sunnah' da hambare shi; kuma kusan duk wanda ya fara kafa wasu ka'idojin faranta wa mabarnata rai da tunaninsa nesa da abin da malamai suke kai ta wannan hanya ya fara fadawa, misali: Ali Hassan al-Halabee da Aboo al-Ma'arabee da ire-irensu.

Salafawa ba su koyar a yi wa wani ta'assubanci ba face Tafarkin Annabta, saboda dalilan aikata haka sun tabbata a kansa; lallai fushinsu idan an taba wanda yake kan Tafarkin Annabta a cikin malamai ko dalibai, yana tasowa ne daga saninsu ga martabar abin da yake dauke da shi na Tafarkin Annabta; ya ci albarkacin abin da yake tare da shi na kyakkyawan tafarki wadanda ake saurin hasararsa, musamman a wannan yanayi da mabarnatan makiraya suka yawaita a kowane lungu da sako.
    
Daga cikin mafi cancantar wadanda ya kamata a buga  misali da su a kan wannan batu shi ne:

Sheikh Rabee Bn Hadee al-Madkhalee [H. A] ya rubuta littafi mai suna:

"التعصب الذميم"

Domin malamai da almajiran da suke kafa tutar kare kansu da malamansu da sabanin gaskiya da adalci; a cikinsa ya nusantar da mabiya Tafarkin Magabata Na Kwarai a kan riko da tafarkin magabatansu na neman gaskiya, da taimakonta tare da ma'abotanta.

Yana daga cikin abin da ambatonsa zai amfanar: Lallai malami ko dalibi yana daukar hanyar bata ce tun daga ranar da ya fara jin shi ma ya kai ya kirkiri wata magana ba tare da wani haske na ilmi da amana ba a jerin maganganun magabata na kwarai [R. A] a kan wata mas'ala daga cikin mas'alolin addini.

Wani zai iya cewa:

"Wannan rufe kofar ijtihadi ne da wayo!"

Sai mu amsa da cewa:

"Mas'alolin addini kala biyu ne:

1. Wacce ijtihadi ba ya shiga cikinta: Ita ce wacce nassi ya tabbata a kanta.

2. Wacce ijtihadi yake shiga cikinta: Ita ce wacce ta rasa nassi a kanta, lallai ma'abota ilmi da amana suna da damar baje gwazonsu domin nemo hukunci a gare ta bisa la'akari da wani dalili da aka yi ittifaki a kansa a matsayin daya daga cikin dalilan Shari'ah.

A kansa: Wanda yake da damar haka fafatawa a wannan fage shi ne Mujtahidi; ba kowane makalli da ido daya ba ga wata mas'ala daga cikin mas'alolin addini: domin sanin abubuwan da mutum zai hada kafin ya taka matakin ijtihadi sai a koma littattafan shari'ah, musamman Usool al-Fiqh, domin sanin hakan zai sa mutum ya tsaya a iya matsayinsa ta fuskar mu'amalantar mas'alolin addini.

A bisa hasken abin da yake sama: Za ka iske an taimaki fanni ijtihadi ne ba rufe shi aka yi ba, za ka ga an kwato shi ne daga hanun masu son hallaka shi ba an kashe shi ba.

A karshe: Kuma haka ba ya nuna kowa ya zama mukallidi, amma zai iya zama mabiya, bayan mun yi bayanin kowane a takaice:

1. Mukallidi: Shi ne wanda addinin malaminsa shi ne nasa, ma'ana: yana koyi ne da malaminsa a kan komai ba tare da sanin dalilansa ba!

Hakika malamai dama sun tafi a kan rashin dacewar haka, a yayin da wasu suke ganin dacewarsa ga gama-garin mutanen da ba su san addini idan sun yi koyi da Malaman Sunnah.

2. Mabiyi: Shi ne mai bin wani malami bisa sanin dalilan da yake kansu tare da tantance su, ta yadda idan ya kuskure gabarin tafarkin gaskiya zai bar shi bayan ya fadakar da shi ya ki gyarawa.

Irin wannan biyayya tana faruwa a tsakanin:

1. Dalibi da malami: Wannan ita ce ta fi faruwa, ta yadda dalibi zai rinka bin tafarkin karantarwa na malamai yana mai la'akari da ingancin dalilan da suke dore a kansu dangane da wasu mas'aloli kafin ya kai matakin ijtihadi, amma wannan ba ya nuna cewa:

i. Sun zama kungiya: Saboda alakar da take tsakaninsu ta addini ce bisa dalili a sakamakon kaiwa mataki na ijtihadi.

ii. Idan dalibi ya kai matakin malunta ya bar la'akari da maganganun malamansa: Hakan ba ya nuna ta'assubanci a gare su, bal dama ilmi wane ya dauka ne daga wajen wane bisa tantancewa da lura.

2. Malami da malami: Ta yadda wani malami zai bi dan uwansa a kan wata mas'ala a cikin mas'alolin addini wacce bai riga ya tsaya a kanta ba.

Kuma abin da ka ji a sama ba ya sauke darajarsa ta malunta, kuma ba shi da alaka da hadin baki ko wani abu da yake da alaka da abubuwan duniya.

A kansa: Kuskure tsammanin hassada da zalunci ga sabawar wani malami ga dan uwansa a sakamakon tsayawarsa a kan ingantaccen dalili a kan wata mas'ala da take karkashin tattaunawa a tsakaninsu, amma akasin haka son zuciya ne.

Wata fa'ida:

Wajibi a kan kowa sanin abubuwan da bai kamata musulmi ya jahilce su dangane da addininsa ba, amma hakan ba ya nuna dole kowa sai ya zama mujtahidi; a yayin da kowane dan hauragiya da bankaura a wannan zamani yake kokarin zama mai fatawa, sai abubuwa suka cakude, har sauran gama-garin mutane suka kasa bambance tsakanin malamai da wasunsu, da Salafawa da Ikhwaniyawa, kuma hakan ya yi sanadiyyar fadawar mafiya yawa a cikinsu ta'assubanci ga barna da ma'abotanta da dan abin da suke tare da shi na ilmi da fahimta.

Allah ya sa mu wanye lafiya.

Ibrahim Lawal Soro
16. 04. 2017 C. E

No comments:

Post a Comment