Ya sharaha a kan harshen mutane, hatta wasu malamai da daliban ilmi, fadin:
"Addini sauki gare shi. "
Da fadin:
"Babu tsanantawa a cikin addini. "
Hakika wadannan kalmomin gaskiya ne, dalilan Shari'ar Musulunci a kansu yawansu ya kai matsayin yanke shakku ga kowane bijirarren 'Dan Zafin Kai' koda Bakhawarije ne, amma idan ya yi amfani da ingantaccen ilmi da tsaftataccen hankali wadanda Allah (S. W. T) ya ba wa Dan Adam domin bambance tsakanin gaskiya da karya, saidai ba shi da su, kuma rashinsu yana sanya bijirewa da bin tafarkin Khawarijawa da sauran kungiyoyi bidi'ah masu tsauraran ra'ayoyi.
Wasu daga cikin wadancan dalilai dangane da wadancan magannu su ne:
1. Fadin Allah (S. W. T) a cikin Soorah al-Haaj (78), ya ce:
"وما جعل عليكم في الدين من حرج"
"Bai sanya muku wani tsanani a cikin addini ba"
Tushe dangane da Shari'ar Musulunci shi ne sassautawa da rashin gallazawa.
2. Da fadinsa a cikin Soorah al-Baqarah (185) (S. W. T):
"يريد الله بكم اليسر ولا يريد بكم العسر"
"Allah yana nufatarku da saukakawa ne, ba ya nufatarku da tsanantawa."
Manema abubuwa masu wahala da tsanani, sun fi kowa saurin bata da lalacewa.
3. Da fadin Manzon Allah (S. A. W) ga Aboo Moosa al-Ash'aree da Mu'az Bn Jabal (R. A) da ya tura zuwa Yemen, kamar yadda ya zo a cikin 'Saheeh' (5773):
"يسرا ولا تعسرا، وبشرا ولا تنفرا"
"Ku saukaka, kar ku tsananta, ku yi bushara, kar ku yi kora"
Asali shi ne saukakawa, amma wani ba shi damar sauke wa wani wata ibada saboda wani nau'i na tsanantawa ya aboce ta, kamar azumi, saida lalura, ita kuma tana da iyakarta.
4. Da fadinsa (S. A. W), kamar yadda ya zo a cikin 'Saheeh' (39), ya ce:
"إن هذا الدين يسر، ولن يشد الدين أحد إلا غلبه"
"Lallai wannan addini sauki ne, kuma ba wanda zai tsananta a cikin addini face (addini) ya samu galaba a kansa"
Wannan hadisi ya kara fito mana da ruhin saukakawa na Shari'ar Musulunci da kyawunta ta yadda ya bayyana rangwame da saukin da ya siffanta da shi idan an yi la'akari da tsarinsa a lokutan da suka shude, saboda haka a rinka tsaiwa a iyakokinsa.
Amma wannan ba ya nuna cewa mutum zai shantake ba zai yi kokarin kaiwa wani mataki a cikinsa ta fuskar imani da aiki ba, fahimtar haka rushe fifikon da ya zo da shi ne da kama tafarkin Murji'ah da sauran yan sharholiya.
Abin da yake rushe waccan munmunan tunani shi ne hadisin 'Umar (R. A) wanda ya sharaha da suna ' Hadisin Jibrilu-حديث جبريل' da ya zo a cikin 'Saheehain' (50) da (8).
A cikinsa Jibrilu ya yi bayani a kan matakan addini uku (3):
1. Musulunci: Wanda yake da rukunai biyar (5) wadanda suka hada aikin zuciya da gabbai, ma'ana: Tauhidi da Akida, Sallah, da Azumi da Zakkah da Hajji.
2. Imani: Wanda yake da rukunai shida (6) da suka kunshi akida.
3. Ihsani: Wanda yake da rukuni daya (1) - a mafi rinjayen maganar malamai- wanda yake da alaka Ayyukan zahiri da badini da suka gabata a matakin farko da na biyu.
Dukkan wadancan matakai ba a kaiwa zuwa gare su sai da kulawa da kwazo, shi ya sa Allah (S. W. T) ya yi alkawarin taimaka wa wanda ya jajirce -ba ya zurfafawa ko ya tsanantawa- a kan tafarkinsa, kamar yadda ya zo a karshen 'Soorah al-Ankaboot' (69), ya ce
"والذين جاهدوا فينا لنهدينهم سبلنا، وإن الله لمع المحسنين"
"Wadanda suka yi kokari (da kazar-kazar) a tafarkinmu lallai za mu shiryar da su hanyarmu (da aikata kwayayawan ayyukan alherinmu) kuma lallai Allah tabbas yana tare da masu kyautatawa"
Har ilau ya tabbata a cikin hadisin Anas Bn Maalik (R. A), kamar yadda ya zo a cikin 'Saheeh' (5774) ya ce: Manzon Allah (S. W. T) ya ce:
"يسروا ولا تعسروا، وسكنوا ولا تنفروا"
"Ku saukaka kar ku matsanta, ku sassauta kar ku yi kora"
-Kalmar 'التسكين' tushen aikin 'سكن' da rubanya harafin 'ك' da ma'anar 'ya kwantar-هدئ' ko 'ya sassauta-خفف' da sauransu.
Ibn al-Hajr (R. A) yana mai fassara wannan hadisi, kamar yadda ya zo a cikin 'Fath al-Baaree' (3), ya ce:
"هو أمر بالتيسير، والمراد به الأخذ بالتسكين تارة وبالتيسير أخرى، من جهة أن التنفير يصاحب المشقة غالبا، وهو ضد التسكين، والتبشير
يصاحب التسكين غالبا، وهو ضد
التنفير"
"Umarni ne da saukakawa, abin da ake nufi da shi riko da sassautawa (ba zafafawa da gasawa ba) a wani lokaci, da kuma sassautawa a wani lokacin na daban, ta fuskar cewa lallai kora tana abotar 'tsanantawa' a galibi, ita kuma kishiyar sassautawa ce, kuma 'bushara' (nasiha da gargadi) tana abotar sassautawa a galibi, ita kuma kishiyar kora ce."
A bisa hasken abin da ya gabata na magana a kan saukakawar Musulunci da Rangwamensa da kuma makalewar wasu mabarnata a karkashinsa nake cewa:
Lallai fadin cewa:
"Addini sauki gare shi"
Ko
"Ba a tsanantawa a cikin addini"
Ba ya nufin mutane su zama masu sakaci da saibi a kan abubuwan da aka farlanta musu, ko aka sunnanta musu, ko aka kwadaita musu, bal yana nufin: Haramcin zurfafawa da tsanantawa a cikinsu ta yadda za su mirginar da ma'abocinsa a kwana-a-tashi.
A takaice: Idan ka duba masu wancan magana za ka iske galibinsu ba su fita daga karkashin wadannan ba:
1. Masu batacciyar Akida da Manhaji: Sune za ka ga suna danganta bacin akidarsu da manhajinsu da saukin addini da Rangwamensa.
2. Masu batacciyar tarbiyya: Wadanda basu da buri sama da yada barna a cikin al'umma, ta yadda idan aka rushe wata barnar tasu sai ka ji sun kammala da fadinsu:
"Addini sauki gare shi"
Da sauran wasu kalmomin gaskiya wadanda suke nufatar dasa barna da su.
Bugu da kari: Na san galibin masu tsanantawa a fagen bidi'ah da son zuciya da sharholiya da sakaci da za su ce wannan zafafawa ce, a sakamakon jahiltar cewa ba zafafawa a cikin riko da abin da Shari'ar Musulunci ta zo da shi bisa iko da iyawa, hakika zafafawa tana cikin:
1. Wuce-gona-da-iri: Kari a kan abin da aka yi umarni da shi.
2. Sakaci: Rashin aikata abin da aka yi umarni da shi.
Sai ya kasance akwai:
1. Zafafawa a cikin kari.
2. Zafafawa a cikin ragi.
Ma'abota wadannan bangarori sune yan tsanantawa!
Ba wanda Shari'ar Musulunci ta goyi bayansa a cikinsu:
Allah (S. W. T) yana mai kashedi da hani ga Ma'abota Littafi a kan zurfafawa a cikin Addini, ya ce:
"قل يا أهل الكتاب لا تغلوا فى دينكم غير الحق"
"Ka ce: "Ya ku ma'abota littafi kar ku zurfafa a cikin addininku (a kan) koma bayan gaskiya"
Ibn Katheer (R. A) yana fassara wannan aya a cikin tafsirinsa ya ce:
"لا تجاوزوا الحد فى اتباع الحق، ولا تطروا من أمرتم بتعظيمه، فتبالغوا فيه حتى تخرجوه عن حيز النبوة إلى مقام الإلهية، كما صنعتم فى المسيح وهو نبي من الأنبياءة، فجعلتموه إلها من دون الله، وما ذاك إلا لإقتدائكم بشيوخكم شيوخ الضلال الذين هم سلفكم ممن ضل قديما"
"Kar ku wuce iyaka a cikin biyayya ga gaskiya, kar ku wuce goda-da-iri a kan wanda aka umarce ku da girmama shi har ku zurfafa a kansa sai kun fitar da shi daga kewayen Annabta zuwa ga matsayin Allantaka kamar yadda kuka yi wa Almasihu, alhali Annabi ne daga cikin Annabawa, amma sai kuka maida shi Abin Bauta koma bayan Allah (S. W. T), kuma haka bai kasance ba sai don koyinku da shehunanku, shehunan bata wadanda suka zama magabatanku a cikin batattu a jiya"
A kansa Manzon Allah (S. A. W), kamar yadda Muslim ya fitar a cikin 'Saheeh' (2815), ya ce:
"قاربوا وسددوا، واعلموا أنه لن ينجو أحدكم بعمله"
"Ku tsayu (a kan ayyukan alheri) kuma ku daidaita, kuma ku sani lallai dayanku ba zai tsira da ayyukansa ba"
Sai Sahabbai (R. A) suka ce:
"ولا أنت يا رسول الله - صلى الله عليه وسلم -؟"
"Koda kai ne ma Ya Manzon Allah (S. A. W)?!"
Sai ya amsa da cewa:
"ولا أنا إلا أن يتغمدني الله برحمة منه وفضل"
"Koda ni ne har sai Allah ya suturce ni da wata rahama daga wajensa da wata falala".
-Ma'anar kalmar 'Kusanci-المقاربة' ita ce tsayuwa a kan ayyukan alheri da nisantar sakankancewa.
-Ma'anar kalmar 'Daidaita-السداد' ita ce tsayuwa a kan ayyukan alheri da dogewa.
Al-Allaamah 'Uthaimeen (R. A) a cikin 'Sharh al-Riyaadh al-Saliheen' yana fassara wannan hadisi, ya ce:
"هذا الحديث يدل على أن الإستقامة على حسب الاستطاعة، وهو قول النبي -صلى الله عليه وسلم-: "قاربوا وسددوا" أي سددوا على الإصابة، أي: احرصوا على أن تكون أعمالكم مصيبة للحق بقدر المستطاع، وذلك لأن الإنسان مهما بلغ من التقوي، فإنه لا بد أن يخطئ كما جاء فى الحديث عن النبي -صلى الله عليه وسلم- قال: "كل بني آدم خطاء، وخير الخطائين التوابون"
"Wannan hadisi yana nuna cewa lallai 'Istiqaamah' (tsayuwa da daidaita) tana kasancewa ce bisa iko da iyawa, kuma fadin Annabi (S. A. W) ne: "Ku tsayu, kuma ku daidaita" ai ku daidaita a kan dacewa: Ku yi kwadayin ayyukanku su kasance datattu da gaskiya gwargwadon iko da iyawa, saboda duk yadda mutum ya kai a tsoron Allah, lallai ba makawa sai ya yi kuskure kamar yadda ya zo daga Manzon Allah (S. A. W): "Duk Dan Adam mai yawan kuskure ne, amma mafi alherin masu kuskure su ne masu yawan tuba"
A karshe: hakika wadancan nassoshi sun bayyana bacin zurfafawa da sakankancewa, kuma sun kara fitowa da Manhajin Ma'abota Sunnah da Hadin kai na kasancewarsu 'Masu Tsakaitawa-وسطيون' amma ba 'Tsakaitawa Ta Zurfafawa' ko 'Tsakaitawa Ta Sakankancewa' ba, saboda wadancan na Yan Bidi'ah da Son Zuciya ne; sune tushen tsanantawa da kausasawa, da Sakaci da sakankancewa, bal 'Tsakaitawarsu a kan gaskiya da aiki da ita gwargwadon iko da iyawa ta kasance'.
Watakila da wannan gajeren rubutu za mu iya dakile wancan sakalci na danganta barna ga addininmu da batun saukakawarsa da sassautawarsa.
Allah ya yi mana tsari da tsanantawa da kausasawa, kuma ka maida masu aikata su kan kyakkyawar turba ta Magabata Na Kwarai da wadanda suka biyo su da kyautatawa.
©Ibrahim Lawal Soro
26. 01. 2017 C. E
No comments:
Post a Comment