A kowane lungu da sako Ikhwaniyawa makirai ne; sun kware a farautar kwakwalen mutane da karya da yaudara, kamar Yan Shi'ah: manufarsu ta Kyautata mu'amala da mutane ko hidimta musu bata wuce su yi shiru garin barnarsu ba, amma matukar za ka bankade ta, sai sun bayyana maka asalin halinsu na kiyatar gaskiya da ma'abotanta.
Wannan kuma shi ne halin galibin yan kungiya da kungiyanci; ka tambaya yi wanda ya yi mu'amala da su, sa'annan ya rabu da su a kan gaskiya, hakika za ka sha labari!
Wani abokina ya taba ban wani labari kamar haka:
"Yan kungiyar kauyenmu suna kira na 'Sheikh' (bai amince da sheikh din da suke kiransa da shi ba, da ya kasance tare da su, kodayake ba Sheikh din ba ne ma), bayan lokacin da suka ga na fara barinsu a sakamakon bacin manhajinsu, sai suka fara kira na 'Ustazu', a karshe ma wasu 'Dan Iska' suke kira na a bayan idona. Laifina shi ne na gane gaskiyar bacin tafarkin raba kan Musulmai da sunan Musulunci!"
Sai na ce masa:
"Haka halinsu yake a ko'ina a duniya, ga su a nan Masar muna ganin irinsu, ba su da aiki sai la'anar Shugabannin Musulunci, da datse mubaya'ar mabiyansu a kansu da cin Zarafin malaman Salafiyyah."
Ka yi taka-tsantsan Ikhwaniyawa a duk lokaci da muhalli da ka tsinci kanka, domin tafarkinsu ya nashe a cikin kungiyoyi masu yawa da suke gefenka, alhali basa cikin Jama'ar Tsira kamar yadda Al-Albaanee (R. A) ya bayyana bayan la'akari da akidunsu da Manhajinsu.
©Ibrahim Lawal Soro
06. 02. 2017 C. E
No comments:
Post a Comment