Sheikh al-Islaam Ibn Taimiyyah (R. A) ya ce:
"المظهرين للإسلام ينقسمون إلى مؤمن ومنافق، والفارق بين المؤمن والمنافق هو : الصدق فإن أساس النفاق الذي يبنى عليه هو الكذب."
"Masu bayyana Musulunci suna rabuwa zuwa Mumini da Munafiki, abin da raba tsakanin mumini da munafiki ita ce: gaskiya, saboda tushen munafurci wanda yake ginuwa a kansa ita ce karya."
Wasu fa'idoji daga cikin maganarsa (R. A) :
1. Musulunci addini ne da yake bukatar bayyanawa, ma'ana: mutum ba zai ce shi Musulmi ba ne amma a ganin alamoninsa a tare da shi, kamar:
i. A lafazinsa da kalmar shahada.
ii. A aikinsa da sallah, da azumi, da zakka da aikin hajji.
iii. A zuciyarsa da imani wanda damshinsa yake bayyana a kan gabbansa.
Allah (S. W. T) ya ce:
"إن الصفا والمروة من شعائر الله، فمن الجح البيت أو اعتمر فلا جناح عليه أن يطوف بهما"
"Lallai Safa da Marwa suna cikin alamomin (addinin) Allah, saboda haka duk wanda ya je hajji ko umara babu laifi a kansa da ya kewaya su (ya yi dawafi a huruminsa)"
Al-Imaam al-Baghwee yana bayyana ma'anar 'Alamomin Allah-شعائر الله' ya ce:
"وشعائر الله أعلام دينه، أصلها من الإشعار، وهو الإعلام، واحدتها شعيرة، وكل ما كان معلما لقربان يتقرب به إلى الله تعالى من صلاة ودعاء وذبيحة فهو شعيرة، فالمطاف، والموقف، والنحر، كلها شعائر الله. "
"Alamomin Allah' sune 'Alamomin Addininsa', asalinta daga 'jiyarwa' ita ce 'sanarwa', tilonta 'alama', dukkan abin da ya kasance sananne domin kusanci da ake kusantar Allah (S. W. T) da shi na sallah, da addu'a da yanka, lalla shi alama ce, haka 'mazagaya' (wajen dawafi), da 'matsaya' (wajen tsaiwar Arfa), da yanka dukkansu alamomin addinin Allah ne".
2. Mumini shi ne wanda ya furta kalmar imani, kuma yake aiki da sakonta, kuma ya kudurce gaskiyarta a zuciyarsa, tare amincewarsa a kan hauhawarsa da karuwar ayyukan alherinsa, kuma da ruguwarsa a sakamakon raguwarsu.
2. Munafiki akasin mumini ne, saidai za su iya haduwa a kan ayyuka na zahiri, kamar:
i. Furta kalmar imani, kamar: Kalmar Shahara da zikirori.
ii. Ayyuka irin na masu imani, kamar: Sallah, da azumi da sauransu.
3. Abin da yake bambance tsakanin mumini da kafiri abubuwa biyu ne:
i. Gaskiya wacce mumini yake riko da ita, kuma ya dora addininsa a kanta.
ii. Karya wacce munafiki yake tafiya a kanta a cikin addininsa, amma yake bayyana sabaninta.
4. Gaskiya tana amfanar da ma'abotanta ta kowace fuska a bangaren addini da rayuwa, ba wanda ya taba rike gaskiya aka ce ya tozarta.
5. Ramin karya kurarrare ne komai zurfinsa; mai bautawa Allah (S. W. T) da karya ya yi mafi girman hasara, saboda ya jijjiga wasu gabbansa kamar muminai, amma ya lalata zuciyarsa, saboda haka ya yi hasarar ladansa, kuma ukubarsa tana jiransa.
Hakika munafurci shi ne tsantsar karya, ita kuma karya ita ce matattarar mushrikai da munafukai.
Allah (S. W. T) ya ce:
"إن المنافقين فى درك الأسفل من النار"
"Lallai munafukai suna madirkaka ta can kasan wuta"
Wadannan sune ma'abota 'munafurci na akida' wadanda suke bayyana karyar Musulunci a kan gabobinsu su boye gaskiyar kafirci a zuciyouonsu.
Amma ma'abota 'munafurci na aiki' wadanda suke aikata wasu ayyuka da aka ambace su da sunan munafurci ko alamarsa, lallai ma'abota manyan laifi ne, idan suka tuba kafin mutuwarsu ana karbar tubarsu, haka ma ma' abota 'munafurci na akida', amma idan sun mutum ba tare da tuba ba, al'amarinsu yana wajen Allah (S. W. T), idan ya so ya azabtar da su da adalcinsa, idan ya so ya yafe musu da falalarsa, sabanin ma'abota 'munafurci na akida' wadanda suke saman mushrikai a azaba.
Allah ya yi mana tsari daga shirka da munafurci.
©Ibrahim Lawal Soro
31. 01. 2017 C. E
No comments:
Post a Comment