Tuesday, 5 March 2024

Manzumar Tauhidi da Akida

 



Gabatarwa


1. Na gode Jallah don Shi ne yake yi min

Baiwa ta komai ba hani za ya min


2. Ƙarin salati ga Nabiyyi Mustafa

Da Alihi Sahabbai nasa ba ƙwafa


Farkon Wajibi a Kan Bayi


3. Sanin Ilahu wajibinka bawa 

Na farko in ka ƙi ka zamto gawa


4. Ko numfashinka ya cike Samaniya

Izza gare ka kan Ƙassai da Maliya


5. "Wa Ma khalaqqul Jinnah" Allah ya ce:

"Wal Insa" sai bauta ka san ka dace.


Wanene Bawa?


6. Duk wani mahluki idonka ke gani

Ƙira shi bawa duk ficensa ya sani


7. Mai hankalinsu akasinsu mumini 

Ko kafiri, da fajiri, da ƙanƙani 


8. Mana ta bawa wata mai biyayya

Ga Jallah donSa kullum ke biyayya


9. Ba shi da tsoron ya wuce ƙiyama 

Ba shi da haushin madara da nama. 


Ma'anar Bauta


10. Bauta sanin abin da Jallah ya ka so

Ya lamance na aiki koda ba ka so


11. Na zahiri da baɗini duk ta haɗa

Da ƙauracewa kishiyarta an faɗa


12. Aikin ibada da cikar soyayya 

Ke yinsa bawa babu yin jayayya


13. Har risinawarsa cikar bautarsa

Da so da ƙi don Jallah ne nufinsa. 


Sharuɗan Bauta


14. Kyan niyya ayyukansa sa ikhlasi

Biyayya gun Manzo da ba iflasi


15. Addini wasu sunka ce ƙwazonsa 

Allah roƙonmu gunka ne baiwarsa.


Matakan Addini 


16. Dinin Islama na da matakai uku 

Ga jerin nan gare ka tamkar ranaku


17. Islamu Addinin Ilahu yai gaba 

Birni da ƙauye ba kamarsa cigaba 


18. Imani shi ne na biyunsu ka ji

Lurarka dai ta zam gare shi ba ji


19. Ihsani shi ne na uku ba tantama

Shi ne ya zo a ƙoli ba mai gardama. 


©Ibrahim Lawal Soro

   09. 09. 2022 CE. 

No comments:

Post a Comment