Wednesday, 6 March 2024

Wata Fa'ida Ta Ibada

 

Daga cikin fa'idojin sallah a cikin jam'i bayan wajabcinta da lada ashirin da biyar da ake samu a mafi rinjayen maganar malamai, lallai akwai wasu fa'idoji kamar haka:


1. Yinta a cikin nutsuwa: Kasancewar sallah ma'abociyar rukunai, da farillai, da sunnoni da mustahabbai yana nuna bukatuwarta zuwa ga nutsuwa wacce ita ma rukuni ce daga cikin rukunanta; rasa ta yana lazimta bacinta.


Hakika ya tabbata duk wanda zai yi sallah a matsayin limami ko mamu yadda yake fuskantar kulawa da lura ya fi yadda yake yi a yayin da yake yin sallah a tilonsa, wannan kuma ya samo asali ne daga:


i. Darajar Sallar ita kanta da  


ii. Nauyin jagoranci da biyayya da yake kan jagora da wanda ake jagoranta ta yadda ya zama wajibi kowa ya sauke wanda yake kansa, shi ya sa aka:


-Umarci limami da sassautawa saboda kar ya fitini mamu da rashin zuwa jam'i a sakamakon tsanantawarsa, kuma aka: 


-Umarci mamu da rashin rigayar limami da wani aiki na sallah, kuma aka yi masa tanadin juyawar fuskarsa fuskar jaki idan ya dauwama a kan wannan aiki har ya zama dabi'arsa.


2. Hadin kan masallata: Idan sun zama madaidaita sahu kamar yadda Manzon Allah [S. A. W] ya karantar a magance da aikace.


3. Mikarwar Limami ga matsakaiciyar rabkanuwar mamu: Amma a yayin da yake karkashin jagorancinsa, saboda abin da yake dauka shi ma na kuskurensa. 


Wannan ya kasance a karkashin wadannan ka'idoji:


i. 'Rabkanuwar mamu limami yana dauke ta'


[وسهو ‏المأموم ‏يتحمله ‏الإمام]‏‏


Amma bisa yanayin da ya gabata da wasu yanayoyi na daban.

 

ii. 'Iyaka an sanya limami ne domin a yi koyi da shi'


[إنما جعل الإمام ليؤتم به]


Saboda haka duk wanda rabkanuwa ta riske shi tare da limami lallai shi ma ta riske.


A takaice: Tabbas fa'idojin sallah a cikin jam'i suna nan yawa, musamman a wannan zamani da yake cike da abubuwan shagaltarwa daga ambaton Allah [S. W. T]. 


A kansa: Idan aka samu sassaucin limami da biyayyar mamu sai ka ga an samu sakamako kamar haka:


1. Ingantacciyar sallah wacce aka kare ta a cikin nishadi da rashin lalaci: Ita ce sallah da aka yi bisa karantarwar Manzon Allah [S. A. W], saboda limami bai tsawaita ba, koda yana tsananta wa kansa a lokacin da yake sallah shi kadai, sa'annan mamu bai kosa ba, koda yana ha'intar kansa a lokacin da yake sallah shi kadai. 


Da hasken abin da yake sama zaka fahimci asalin abin da ya sa wasu mamu suke fada da limamai, haka ma wasu limamai suke korafi a kan wasu mamu.


Allah ya yi mana baiwar lazimtar sallar jam'i. 


Ibrahim Lawal Soro

06. 02. 2017 C. E

No comments:

Post a Comment