Tuesday, 5 March 2024

Warware Wata Shubuha

 

Hakika takaita kafa hujja a kan Kur'ani, da Sunnah da Ijma'i domin hukunci ga mutane, musamman 'Yan Bidi'ah da Son Zuciya, sabuwar hanya ce da Yan 'Ruwantar da Tafarkin Salafiyyah' [المميعة‎]‎ suka dauka domin shigo da kowane mabarnaci cikin da'irar Salafiyyah, kodayake dama suna da bahaguwar ka'idan nan ta:


‏"‏المنهج واسع" 


"Manhaji fadi gare shi"


Ma'ana: Zai iya dauke Salafawa da wasunsu. 


Idan ka yi la'akari ba za ka iske wani bambanci a tsakanin wannan ka'ida da ka'idar Ikhwaniyawa da suke yi mata lakabi da 'Ka'idar Zinariya' [القاعدة ‏الذهبية‎]‎ wacce mutuncinta bai kai a kira ta 'Ka'idar bakin karfe' [القاعدة ‏الحديدية‎]‎ ba, saboda an rawaito daura aure da shi a zamanin Manzon Allah [S. A. W], amma tasu ka'idar in banda sanadiyyar mutuwar aurarraki ba abin da take yi, saboda anke hukuncin kisa ga wasu a sakamakonta, kamar yadda aka yi daurin rai-da-rai ga wasu a sakamakonta, ka ga wadannan abubuwa ne da za su bayu zuwa ga karewar aure, idan ma ba a yi la'akari da matan da suka gujewa mazajensu ba a sakamakonta.


Mafi girman misali da zai bayyana maka ha'incin wadancan mutane karara shi ne:


Idan wani musulmi ya aikata bidi'ah sai an nemo aya a cikin 'Littafi' da hadisi a cikin 'Sunnah' wadanda suke nuna cewa shi da kansa Bidi'ah ne a nassance, kuma ba za a yi wa mai shi hukunci da bidi'ah ba koda an tsayar masa da hujja, a bisa rinjayayyen ra'ayi a wajen Ma'abota Sunnah, sai an samu Ijma'i.


Idan an rasa aya ko hadisi kuma dole malamai su yi ijma'i a kan bidi'ancinsa kafin a yarda cewa dan bidi'ah ne; ka ga ba wanda zai fadi haka sai dayan biyu: 


1. Jahili: Idan ya zama mai matsakaicin jahilci idan an karantar da shi zai iya alkinta.


2. Dan Son Zuciya: Wanda tabewa ta yi masa kanta babu wata hanyar daidaitawa da shi.


Hatsarin da yake cikin wannan motsi ne: Idan aka biye irinsa zai zamanto ba wani Dan Bidi'ah a wannan zamani -ba burin kowa ya zama halakakke ba, amma tabbas halaka ta tabbata ga wasu, Allah ya kare mu gaba daya- sai irin na baya, kamar: Khawarijawa, da Shi'ah, da Mu'utazilawa, da Murji'awa da  sauransu.


A sallama bisa jidali ba wasu Kungiyoyin Bidi'ah sai su, tunda a wajensu Ikhwaniyawa da Tablighawa ba Yan Bidi'ah ba ne, duk da Malaman Sunnah irin al-Albaanee [R. A] sun tabbatar da cewa: Yan Bidi'ah ne, mai zai hana wani Malamin Sunnah amfani da 'Qiyaasi' matukar an samu illa domin tabbatar da bidi'ancin wata kungiya daga cikin kungiyoyin zamani?


Ko Malamin ya yi 'Ististinbadi' a cikin ingantattun dalilan hukunce-hukunce domin ya  tabbatar da irinsa a kan wanda ya cancance shi?


Ko wata 'Maslahah' ta sa ya yi amfani da sabanin abin da aka sani domin tunkude wata babbar barna?!


Kuma duk hakan ya kasance a karkashin amincewarsa da wadancan kungiyoyin a matsayin tushen bidi'ah da son zuciya a tsakanin Musulmai?!


Domin fuskoki da na ambata na tabbatar da wasu hukunce-hukuncen Shari'ah da koma bayan Littafi, da Sunnah da Ijma'i su fito maka fili, zan so ka rike wadannan a matsayin misali: 


1. Kiyasin kungiyar al-Qa'idah da ISIS da Khawarijawa, saboda tabbatar illoli a tsakaninsu wadanda wasunsu suka bayyana a cikin wadannan munanan ayyuka:


i. Fita daga cikin al'ummar musulunci.


ii. Kafirta Musulmi don ya aikata sabon da ba shirka ba, kuma ba tare da ya halatta shi ba.


iii. Kashe Musulmai da barin kafirai da sunan farawa da arnan gida kafin na daji.


vi. Sanya tsoro da firgici a zuciyoyin al'umma tare da yi musu sata da kwace.


v. Tada zaune-tsaye a cikin al'umma ta hanyar zanga-zanga, da zaman-dirshan, da tafiye-tafiye da sauransu.


Ka ga wadannan kadan ne daga cikin ayyuka da siffofin Khawarijawa, kuma sune illolin da suka hada wadancan kungiyoyi biyu da na ambata da su. 


A karkashin abin da ya gabata babu laifi wani malami da ya ga irin wadancan siffofi da illoli a tare da al-Qa'idah da ISIS ya kira su Khawarijawa, idan ya ga dama ya takaita da fadinsa: Yan Bidi'ah, ko wani abu makamancin haka. 


Kari a kan haka: Boko-Haram ma Khawarijawa ne, na taba fadin haka a September ta 2013 wancan dan son zuciya ya yi min inkari, saboda na saba wa ra'ayinsu na karyata kiyasi da makirin salo. 


2. Babu laifi a yi 'Istinbadin' hukunce-hukunce kamar haka:


i. Rashin dorewa da cin nasara. 


ii. Alamar munmunar makoma da rashin dacewa.


iii. Wauta da karancin fahimta da gurbacewarta. 


Ga Khawarijawa da wadanda suke kan irin tafarkinsu a karkashin siffofi biyu da Manzon Allah [S. A. W] ya labarta dangane da su a cikin ingantaccen hadisi:


‏"‏حدثاء الأسنان سفهاء الأحلام"


"Masu karancin shekaru ne, kuma masu wawayen tunani"


Ka ga wadancan hukunce-hukunce sun dace da wadanda suka siffanta da wadannan siffofi da Manzon Allah [S. A. W] ya danganta da su, saboda haka ba wanda zai musanta irin wannan tabbataccen al'amari a Shari'ah sai wanda ambatonsa ya shude ba tare da jimawa ba.  

 

3. Za a iya amfani da yi wa mutane Jarabawa a kan sunnancinsu da wadanda suka yi shuhura da bankade halin yan bidi'ah da son zuciya a gwargwadon yadda maslaha ta hukunta; kamar yadda Magabata Na Kwarai suka yi, musamman wadanda ba a rufa-rufa a kan kiyayya da su, kuma wannan ba ya nuna rataye sunnancin wani da su, amma yana lazimta cewa: Inda ba su da matsala a cikin sunnancinsu me zai sa su rinka kiyayya ta addini a zahiri da su a matsayinsu na jagororin Sunnah?!


Saboda haka: Masu irin wannan hali su suka fi cancanta da wadannan siffofi:


1. Zurfafawa: Ta bayyana a cikin kariyar da suke bayarwa ga Yan Bidi'ah da Son Zuciya ta hanyar takaita hukunci da dalilan Shari'ah guda uku [3] kacal a yayin hukunci ga mutane, bal shu'umancinsu ya kai mataki na tawilin dalilan da suka takaita wasunsu bisa ha'inci, idan an yi amfani da su a kan wadanda soyayyarsu ga ta barna ta kasance daya.


A matsayin kammalawa: Lallai Ma'abota Sunnah da Hadin Kai na gaskiya suna amfani dukkan dalilan da aka yi Ittifaki a kan amfani da su domin tabbatar da wani hukunci na Shari'ah, kuma ba sa tsegumi a kan wanda ya yi amfani da wanda aka yi sabani a kansa, matukar sabanin yana da wani sashi na abin la'akari a cikinsa, domin sanin irin wadancan dalilai sai ka koma littattafan 'Usool al-Fiqh' wadanda aka rubuta su a kan Tafarkin Annabta.


 Ya Allah ka bankade wa mutune munin halinsu domin tsira daga talabobuwarsu! 


Ibrahim Lawal Soro

21. 04. 2017 C. E

No comments:

Post a Comment