Manzumar Tauhudi da Aƙida (2)
Ma'anar Musulunci
20. Ma'anar miƙa kai ga Jallah shi kaɗai
Lura da ɗa'a shirka i mata wadai
21. Da kore duk bautar wani Ilahu
Roƙonsa fata jingino Allahu.
Rukunan Musulunci
22. Shahada ce a farko sai ko Salla
Mai binsu Zakka azumi ka kalla
23. Ƙarshensu Hajju mai iko yana tafe
In ka riƙe su rayuwarka ƙarfafe
24. Amma na farko shi ne dai mabuɗi
Dominsa yaƙi anka tsaida ba haɗi
25. Mai rushe ɗansa ya rushe dininsa
Ƙimarka kare dukka martabarsa
Sharuɗan Shahada
26. Ka san manarta sai ka san sukuni
A farko sai yaƙini anka nuni
27. Kula a zuci zahiri gare ta
Karɓarka duk hukunci da batunta
28. Ihlasi a cikinsu na da ambato
Sai gaskiya ta zuci babu yin zato
29. Ka so ka ƙi dominta don fitarka
Sharɗanta bakwai sunka zo gare ka.
Manzumar Tauhidi da Aƙida (3)
Ma'anar Imani
30. Manar imani aiki ce da furuci
Furci na zuci harce zo ga tsokaci
31. Aiki na zuci harce har da gaɓɓai
Ƙarinsa da ragi ko tabbas ba wai
32. Biyayya ce take kai shi samaniya
Saɓo ko ƙas ke kai shi can cikin wuya.
33. Da shi fikonka ke zama ga ɗan uwa
Ba tantama halinsa ne ko hauhawa
34. Imani shi ne gaskatar Ilahu
Mala'iku da Littafan Allahu
35. Ranar Ƙiyama Manzanni da Ƙaddara
Ta hairi sharri dukka dai ya tattara.
Kashe-kashen Tauhidi
36. Tauhidi na da nau'uka guda ukku
Gare ka za ni zayyano da babbaƙu
37. Nau'i na farko Tauhidin Ibadati
Kaɗaita Jallah kar ka yo ta'annuti
38. Kaɗaita Allah da batun halitta
Da arziƙi da nau'ukan bajinta
39. Shi ya biyo shi babu mai jaya da shi
Sai na ukunsu kar mu yo wasa da shi
40. Kaɗaita Allah a cikin siffa taSa
Da sunaye da ayyukan kama taSa.
©Ibrahim Lawal Soro
11. 09. 2022 CE.
No comments:
Post a Comment