Tuesday, 5 March 2024

Rayuwa

 Rayuwa tsuntuwa ce a gafaƙar lokaci

Kamar rairayi ta ke 

Ta fi zabi tashi

Rayuwa ta rai ce

Ba ta samuwa sai da uwa

Jagoranta ruwa

Tushen duk wani arziƙi


Rayuwa ita ma ƙofatanninta

Na ƙetara dajukan makwanni

Ita ma faratanunta 

Na nome kwanaki a fagenta

Ta fi zuciya ƙaulani

Ta fi hawainiya sauyi 

Ta yi kama da rariya mai giɓi

Ta fi masa son juyi

Rayuwa ita ce sambatun bebe

Mai ɗaga hankalin sauraro! 


Rayuwa mai daɗi

Ilmi  kan zamo sukarinta

Tabbatacce da ake ganin tasirinsa

A sakamakon aiki

Ilmi yake haskawa. 


Furannin rayuwa kwanaki

Tsadarsu ta fi azurfa da zinare

Wane Bitcoin balle PI

Kuɗi dare ɗaya 

A tunanin Jajurtattu

Matasa masu kazar-kazar 

A duniyar tsammani! 


Rayuwa kin mani komai

Da ba su buƙatar kome

A tsarukan masu wadata! 


Ƙi ƙaddara kin ɗaukaka ni

Ba zan kasance Malaki ba!


Ƙi ƙaddara kin sauƙe ni

Ba zan gaza amsa ƙiran Malam ba! 


Rayuwa afuwa tata bacci

Mai ɗauke jarumi a filin daga

Mai kwance naƙuda da mafarki! 


Rayuwa ko kin humbe ni 

Na dade da kammala aikin

Da ba za ki lalatan ba! 

Don na kasance cikin maƙiyanki

Masu tanadin rushe ki

Kafin na yo dakon ajalina! 


No comments:

Post a Comment