Hakika Manhajin Salafiyyah ya yi hanun riga da ha'intar al'umma, kamar:
1. Rarraba Kan Al'ummah: Saboda Manhaji ne da yake dore a kan hada kan Al'umma a kan mafi alherin Manhaji.
Allah (S. W. T) ya ce:
"واعتصموا بحبل الله جميعا ولا تفرقوا. "
"Ku yi riko da igiyar Allah gaba dayanku, kar ku rarraba. "
Kuma manhaji ne da yake tsoron rashin kasancewa tare da Manzon Allah (S. A. W) a karkashin fadin Allah (S. W. T):
"ان الذين فرقوا دينهم وكانوا شيعا لست منهم في شيء. "
"Lallai wadanda suka rarraba (a cikin) addininsu, kuma suka kasance kungiya-kungiya ba ka tare da su a kan wani abu (na alheri)."
2. Raunata Al'ummah: Ta hanyar rashin karantar da ita abin da zai zama alheri ga duniyarta da lahirarta, kana da hidimta mata.
Manzon Allah (S.W. T) ya ce:
"خير الناس من ينفع الناس. "
"Mafi alherin mutane shi ne wanda yake amfanar mutane. "
Da fadinsa (S. A. W):
"خيركم خيركم لاهله، وانا خيركم لاهلي. "
"Mafi alherinku shi ne mafi alheri ga iyalansa, ni ne mafi alherinku ga iyalai na."
A bisa hasken hadisi na farko za mu fahimci cewa: Lallai Salafawa sune mafi alherin mutane ga mutane, a sakamakon hidimarsu gare su, daga cikin ire-irenta akwai:
a. Bankade halin wadanda suka lulluba da mayafin Sunnah alhali ba ma'abotansa ba ne, bal sun suturta da shi ne domin su yake shi daga ciki.
Mafi hatsarin mahara shi ne mahari gare ka daga cikin gidanka.
b. Martani Ga Wadanda Suka Saba Wa Kyakkyawan Manhajin Magabata Na Kwarai: Wannan babban aiki ne a fanni umarni da kyakkyawan aiki da hani gabarin mummunansa, bal ba kowa Allah (S. W. T) yake azurta shi da kwazon tsayuwa da shi ba sai zababbu daga cikin Ma'abota Ilmi da Kafaffun Almajiransu.
A bisa hanken hadisi na biyu kuma za mu fahimci kasancewa mafi alherin mutane yana da alaka da kyautata wa iyalai, kuma ba mafi girman kyauta da mutum zai yi wa iyalansa sama da kokarin dora su a kan Tsayayyen Tauhidi, da Tsaftatacciyar Akida da Ingantaccen Manhaji, kuma ba wanda ya aikata haka ga iyalansa ya fin Manzon Allah (S. A. W) da Wadanda suka biyo Manhajinsa da Kyautatawa: Suna kokarin wayar da kan al'umma dare da rana a kan al'amuran ingantaccen addinin Allah (S. W. T) wanda ya barranta daga Shirka karama da babba, ko Bidi'ah Mai Kafirtarwa Ko Fasikantarwa, ko Sabo Babbansa da Karaminsa.
A takaice: Salafiyyah aminci ce ga Al'umma, idan Salafawa suka kare a cikin Al'umma abubuwan da ake tsammanta mata na azaba zai iske ta.
Kari a kan haka: Kamar yadda Sahabban Manzon Allah (S. A. W) suka zama aminci ga wannan al'umma haka Salafawa suka zama aminci gare ta, saboda dalilai kamar haka:
1. Sune mabiya Manhajin Sahabbai na hakika.
2. Sun fi kowa kare martabarsu, idan kana son tabbatar da wannan batu sai ka tambayi Yan Shi'ah, saboda ba wadanda suke kwasar kashinsu a hanunsu koma bayansu.
3. Sune masu tsayawa a kan Manhajinsu dangane da kowane batu, kamar:
a. Hakuri da zaluncin shugabanni.
b. Da'a gare su a kan abin da bai zama sabo ba.
c. Ganin rashin halaccin fito-na-fito da su da kalma ko makami.
3. Munmunan Wakilci Gare Ta: Ta hanyar assasa kungiyoyin da za a zage ta da su, kamar yadda hakan yake faruwa dangane da kungiyoyin Yan Bidi'ah da Son Zuciya.
A karshe: Lallai halin ha'intar al'umma da rashin bayyana mata kyakkyawan tafarkin da tafiyarta a kansa ya zama wajibi ba na Salafawa ba ne, bal suna ganin halaccin ukuba ga mai aikata haka.
Sheikh al-Islaam Ibn Tamiyyah (R. A) yana mai bayanin maha'intan da suke kare Manhajin Yan Bidi'ah da Son Zuciya tare da bayyana ukubarsu a cikin 'Majmoo' (2/133) ya ce:
"ومن كان محسنا للظن بهم وادعي انه لم يعرف حالهم؛ عرف حالهم، فان لم يباينهم، ويظهر لهم الانكار، والا الحق بهم، وجعل منهم. "
"Duk wanda ya kasance mai kyautata tsammani a gare su, kuma ya raya cewa bai san halinsu ba; sai a sanar da shi halinsu, idan kuma ya ki nisantarsu, kuma ya ki bayyana musantawa gare su, (in ba haka ba) sai a hada shi da su, kuma a maida shi (daya) daga cikinsa. "
Wasu Fa'idojin daga cikin maganarsa:
1. Ba a kyautata zato ga Yan Bidi'ah da Son Zuciya bisa bidi'arsu.
2. Wanda ya nuna bai san abin da suke kai na bata ba za a bayyana masa, idan ya juya gabarinsa za a hade shi da su, wannan shi ake kira: 'Bidi'antarwa Da Abota' 'التبديع بالصحبة', kuma Magabata Na Kwarai sun yi ijma'i a kan zantuwarsa.
Manzon Allah (S.A.W) ya ce:
"المرء هلي دين خليله، فلينظر احدكم من يخالل. "
"Mutum yana kan addinin badadinsa , (saboda haka) dayanku (kowannenku) sai rinka duba (addinin) wanda zai badadanta (abota)."
Abd Allah Bn Mas'uud (R. A), kamar yadda ya zo a cikin 'Al'Ibaanah' (502) ya ce:
"اعتبروا الناس باخدانهم، المسلم يتبع المسلم، والفاجر يتبع الفاجر. "
"Ku la'akarci mutane da abokansu, Musulmi yana bin Musulmi, fajiri yana bin fajiri. "
Ya kara da cewa:
"انما يماشي الرجل ويصاحب من يحبه ومن هو مثله. "
"Iyaka mutum yana tafiya da abotar wanda yake so ne, kuma da wanda ya kasance kamarsa. "
Al-Imaam al-Auzaa'ee (R. A), kamar yadda ya zo a cikin 'Al'Ibaanah' (420) ya ce:
"من ستر عنا بدعته، لم تخف عنا الفته. "
"Duk wanda ya boye mana bidi'arsa, (lallai) abotarsa ba za ta buya mana ba. "
A karkashin wadannan bayyanannun dalilai nake cewa: Duk wanda yake cewa shi ba dan wata kungiya ba ce, amma bayyananniyar abotarsa da zababbiyar zamantakewarsa
da yayanta yake yi lallai danta ne, saboda aikin mutum shi yake fassara boyayyen halinsa.
3. Daga cikin hanyoyin barranta gabarin Bidi'ah da Yayanta akwai:
a. Inkarin abin da ma'abotanta suke aikatawa.
b. Da bayyana nisantarsa gabarin tafarkinsu a aikace.
A kansa: Duk wanda ya gaza aikata dayan biyun wadannan tare da samuwar karfin haka bai zama kowa ba face kirgagge a cikinsu, saboda shirunsa tamkar amincewa ce ga sabawarsu.
Ilmi yana wajen Allah (S. W. T), kuma muna rokon kari daga falalarsa.
©Ibrahim Lawal Soro
29.02.2016 C. E
No comments:
Post a Comment